💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰
*TUKUICI GA:* sweetheart😘
*SHAFI NA 5📑*
*__________📖* A kasan sallaya ta ganshi da'alama sallah yayi bacci ya dauke Shi ganin Idan sa a rufe ajje abincin tayi a kusa da shi ta dauki jakar ta tasa biro da extra book a ciki ta hada da uniform din ta ta ajje akan gado sannan ta wuce toilet da hijibi a jikin ta.
Har ta fito Yana nan kwance be motsa ba daga inda yake wurin madubi ta wuce ta a hankali take shafawa wai dan kar ya tashi komai ahankali yake yin sa har ta gama ta dauki uniform din ta ta Shiga toilet tasa ka sannan ta fito ta cire hijabin dake jikin ta tasa wani Karami ta kalle Shi ta kalli agogo ganin 8:30.
Tace, "Kai haka lokaci yaja ban Sani ba? To tashi zaka yi kaci abinci sannan Ka tafi in case Kar wani ya shigo".
Wurin sa ta karasa ta zauna a gaban sa inda ta ajje abincin hannu tasa akan goshin sa da niyyar tashin sa taji wani zafi na zazzabi ta daura a wuyan sa namma de zazzabin ne.
Tashi tayi ta sauka kasa dakin Mujahid ta nufa babu knob daman ita a tsarin ta bare kuma sallama indai ba dakin Daddy ko Mama zata je ba sunyi jarabar sunyi mitar duk a banza Mama tayi ta bari haka ma Daddy, daman tasan yana bacci yanzu tashin sa ta fara yi."Ya mujahid, ya mujahid de Ka tashi Dan Allah".
Bude idan sa yayi ya bata fuska.
yace, "Meye?"Cuno baki tayi ta fara wasa da hannun ta.
Tace, "Magani zaka bani zazzabi zazzabi nake ji tun jiya"."Mtsww kuma ni Zan Baki? Kije ki dauka mana a dakin Mama".
"Tafa rufe dakin ta kuma bansan wanne da wanne zan sha ba jiya fa kusam dashi na kwana".
Be kara magana ba dan yasan bata san zazzabi ya rufe ta shiyasa tana jin ko ciwon Kai ne take shan magani idan ya kama ta be iya Mata da sauki ba, tashi yayi ya dauki mukullai ya fito daga dakin tana biye dashi har suka hau sama dakin Mama drawern da suke ajje magani ya Bude ya harhado mata da dose din Wanda zata sha na yau Yana miko mata ganin bata ansa ba yasa shi juyo wa ya kalle ta ganin ta yayi sai bincike take mata a daki sai wacce tayi mata ajiya.
Yace, "ke! Bincike ko? Cigaba tou sai na fada mata".
Dawowa wurin sa tayi ansa tana wani tura baki tana kumbara shi.
Tace, "wannan fa nake nema immm wannan yama? Tuna min".
Harara ya wurga mata Yana rufe drawern yayi gaba itama fitowa tayi sai da ya rufe suna sauko.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...