🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•**SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''
*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 59📑*
*__________📖* Yau tunda ta tashi ta nufi jeji dan tayi casa sai dai tana zuwa taga har anyi nata an basu kud'in sun raba ba abin tayi magana ba a fara mata gori haka ta juyo gwanin ban tausayi ta k'ara ya mushewa ta jeme ta rame sosai tsufa nan ya fito ga kaya datti dan sam bata iya wanki sosai sai dai ta jik'a su kawai ta tsame su ba kullum take jurar darzar kaya ba tana zuwa gida taga sauran abincin da yara suka ci tambaya tayi ko a kwai aka ce babu, haka ta zauna ta fara cin sauran abincin yara haka ta zauna ta fara ci tana ci ta wani hawaye ya zubo a idan ta tasa hannu ta share taji ance.
"Indai rayuwa ce yanzu kika fara gani a haka kuma zaki k'are kiyi addu'a d'anki yazo wurin gawarki".
Da ido tabi wacce tayi maganar har ta shiga 'yar bukkar ta, mai gidan ne ya zo hannun sa rik'e da leda ya samu waje a kusa da ita gefen tabarmar.
Yace, "Hajjaty sannu da gida".
"Sannu".
"Yawwa Shugaba ne ya bani sak'o yace na kawo maki".
Ya fad'a yana mik'a mata ledan, ta ansa ya tashi ya tafi, jiki na rawa tasa hannu ta bud'e ledan kaya ne Kala uku taliya guda biyu sai shinkafa da sabulun wanki duka d'ai d'ai da kud'i dubu d'aya.
Kud'in ta d'auka ta d'aga bata san sanda wani hawayen ya zubo mata ba, bata ankaraba taji an fizge kud'in wata ce ta ansa da ido ta bita.
Tace, "Daman kin ranci kud'i na ko kin manta? dan haka a kud'in nan zan baki d'ari d'ari ne kawai sau biyu sauran kuwa nawa ne, d'ari takwas kika ara ina irgawa daman sai da aka ce kada na baki na baki hamsin hamsin ba wasa bane".
Ko gama jin k'amshin kud'in batayi ba aka karb'a kuma wai za'a bata d'ari d'ari sau biyu? shima ba'a tare ba? maganar ta taji tana dawo mata sabuwa fil acikin kunne.
"ina raye babu mai bashi kud'i naira d'ari ta ishe shi".
Ta tuna wannan maganar ta ta a sanda zai fara zuwa makaranta, hawayen da ke zuba ne a fuskar ta ne ya k'ara gudu tasa hannu ta share shi tana jan majina ta bud'e sauran kayan ta gani shinkafar ma ko kwano bata kai ba k'ara goge hawayen ta tayi tana kallan kayan can taga wata farar takarda ta d'auka.
"Ina so ki zama mutum ne, kisan yarda ake zama da mutane da'ace kin iya zama da mutane da duk abinda yake samun ki be sameki ba, d'an ki ya matso sosai akan rashin ganin ki da beyi ba dan haka nace masa kina nan k'auye kina yin zumunci ya kuma aminta dan nace masa kince kinfi jin dad'in zama nan kada ma kiyi fushi dashi besan komai ba game da wannan ki zauna ki cigaba da masa addu'a".
Jikin tane yayi wani irin sanyi ashe duk abinda take ciki be sani ba.
Haka ta gama kukan ta kwanin ban tausayi ta tashi ga zazzab'i da take ji tun jiya amma ba halin fad'awa kowa, haka ta kwanta akan tsummar katifar ta da kuma kayan ta yanzu jakar ma anfi k'arfin ta an kwace ta daga wurin ta, tana kwanciya lokacin Azahar yayi gashi ruwan alwalar ma sai ta d'ebo ta tashi ta fita taga ruwa a bucket kawai ta fara alwala da sauri gudun kada a ganta sai dai tana idar wa mai ruwan na zuwa.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...