*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 23📑*
*__________📖* Yana zaune taje ta same shi bayan ta dai-dai ci lokacin gama news yayi.
Yace, "ya sunan Baban yarinyar?"
"Hussain Ahmad su d'in 'yan Gombe ne aiki ya kawo su Kano".
Jinjina kai yayi yana kallan tv ita kuma tana kallan shi.
Yace, "wanne unguwa suke anan?"
"Shine bansani ba ban tambaya ba kuma".
"To shikenan zan sanar da su Shehu sai su zo su nema masa auran ita yarinyar".
"Wanne shehu kuma?"
Kallan ta yayi ya d'auke kai.
Yace, "ina da wani shehu bayan shi ne?"
Yarda ya kalle ta da yarda yayi maganar ne yasa ta girgiza kai.
Tace, "a'a baka dashi".
"Amma gani nayi kamar yayi nisa yaushe suka taso daga kebbi zuwa Kano? ai nisan dayawa".
"Sanda suka zo nemar wa Auwal aure meyasa baki ce yayi nisa ba sai yanzu?"
Zuciyar ta taji ta buga shiga haka saurin gano mutum da wuri duk kuwa basajar mutum shi ba ruwan sa yanzu nan zai gano ka.
Tace, "bakomai dayake nazaci abin da gaggawa ne amma zan fad'a masa".
"Ki fad'a masa me fa?"
Yana kallan ta yayi maganar hakan yasa tayi murmushi mai kyau.
Tace, "za'a d'an jin kirta wai".
Maida kansa yayi zuwa tv.
Yace, "Nan da wani satin za'aje Insha Allah bama sauri kinsan da haka".
"Hakan ma yayi Allah ya saka da alkhairi".
"Amin".
Ummi ce ta fito sanye cikin kana nan kaya kan ta ba d'an kwali kallan ta yayi.
Yace, "Ummi the next time na kara ganin ki with this cloth Allah sai ranki ya 'ba ci sosai".
Yana rufe baki ta koma inda ta fito.
Yace, "Bana ganin laifin kowa sai naki For God sake kina ganin yarinyar ta fito da k'anan kaya ga Maza a gida amma bazaki iya bata magana ba".
"Abban Ummi gani nayi har yanzu ita d'in yarinya ce dudu shekarun nata nawa suke? Kuma ai mazan 'yan uwan ta ne fa ciki d'aya suka fito".
"Yarinya ko? su masu aikin maza ba maza bane hmmm kada ki hana ta to tunda har yanzu she's a girl".
"Dad'i na dakai saurin hawa wallahi kayi hakuri to shikenan".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...