10

112 14 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023











*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰

*TUKUICI GA:* sweetheart😘

*SHAFI NA 10📑*

*__________📖* Washegari ta kama Alhamis inda ya shirya cikin kayan sa Mai squeezing abin beda ko naira biyar da zai sai jotter da pen Shi da yayi agriculture zai koma medicine abin Yana bashi mamaki hakan sa ya shirya ya fita part din Daada ya Shiga Wanda dudu Shigar befi sau daya ba wannan shine na biyu Yana Shiga yaga Hajjaty zaune shikuma Yana kasa Yana breakfast ba sallama daman Shi a tsarin sa ya zauna a kasa.

Yace, "Daada kudin mota".

"Uwar Ka ce ta bashi da zai Baka?"

Hajjaty ta fada tana hararan shi.

Daada yace, "Hajjatyyyy".

Yarda ya Fadi Hajjatyn yasa ta kallan Shi irin kallan me nake ji.

"Kai saddik Ka kiyani daga cewa uwar sa? Shine zaka wani kira suna na da karfi irin gardadi ka kemin Kenan? To wallahi mutakar ina Raye babu Kai babu bashi kudi koda kuwa matar Ka ce kudi de naira dari ta ishe Shi".

Yarda ya sunkuyar da Kan sa be dago ya kalle ta balle yaga yarda take fada tana wani hura yanci Yana ya tsina fuska.

Daada cikin muryan tausasa harshe.

Yace, "Hajjaty Mai zai hana a bashi koda kullum duba daya ne".

Zabura tayi kamar Wanda taga abun tsoro.

Tace, "saddik kana da hankali kuwa? Duba fa. Ahhh! Kawai kace shikenan mashayar Shan giya zai fara daga nan kuma kullum yake dawo min gida a buge daga nan kuma ya fara laka da min na jaki shikenan he will ruin my  life".

"Haba Hajjaty kama ta yayi ace muna masa fata nagari sai kiga..."

"Yi min wa'azi nace kamin wa'azi tunda ni bansan dai-dai ba bansan ya kama ta me kasani Kai kana can Ka baza hanci a office ni kuma na barni a gida ina fama dashi".

"Yi hakuri". 

Daada ya fada ya koma Yana kallan abincin da ya fara ci shigowar sa yasa Shi ya dai na yanzu kuma kwata kwata abincin ya fita a  ransa.

"Simple instruction baza'a bi ba Kar ayi kaza to shikenan Amma a'a bade Kai ba idan nace kaza sai Kabi wata maganar kayi jayayya dani matar Ka ta koya maka".

"Kiyi hakuri".

"Bashi ya tafi".

Hannu yasa a aljihu fito da 'yan dari biyar biyar babu canji hakan yasa ya miko masa dari biyar ta wafce.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now