*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 16📑*
*__________📖*Ranar babu Wanda ya fita a cikin su har Daddy ta Kanas yaje har wurin aikin sa ya dauki hutun satin daya dake be fiye neman hutu ba kome za'ayi Yana zuwa aikin sa kuma akan lokaci baya makara, Yana nema aka bashi bugu da Kari kuma ranar Friday dayazo kamar marar lafiya hakan yasa ko tambayar ba'asi ba'ayi ba aka bashi.
Ba ita ta farka ba sai karfe daya duk jikin ta ciwo yake mata ga wani Zazzabi da take ji, bude idan ta tayi ta ware su tsab a Kan su suna zaune a kasa har Daddy suna cin abinci Mama bata nan kallan su kawai take kafin ta yunkura ta tashi zaune.
Daddy yace, "Kauwa ta kin tashi?"
Daga masa kai alamar eh.
"Kiyi wanka kiyi sallah ko?"
Namma daga masa kai tayi.
"Mujahid Kai da Baffa Maza ku taimaka mata Ku kaita dakin ta".
Tsayawa sukayi da cin abincin suna kallan ta.
Mujahid yace, "Daddy Bari to mu karasa cin abincin?"
"Aww jayayya zakayi dani?"
Baffa yace, "a,a Daddy nufin sa fa mu Ida cinye lomar nan".
Kwafa Yayi ya cigaba da acin abincin sa.
Ba yarda suka iya haka suka je suka taimaka mata har dakin ta a Kan gado suka ajje ta, ta Galla musu harara.
Mujahid yace, "mu kike harara?"
Aikuwa ta fashe da kuka, matsowa suka yi zasu ba'asai ta fara dukan su tana kuka duk da bawani zafi bane da dukan amma sun ji mamaki.
Baffa yace, "ke ranki zai baci".
"To duk Baku bane kuka sa aka sace ni du laifin kune ai".
Ta karashe tare da kwantowa kan Mujahid dake daf da ita.
"Siyama me kike so ki fada?"
Tasowa cike da hargowa.
Tace, "ehh mana ya Baffa Akan wasu ne 'yan makarantar ku kai da Ya mujahid Sabida Ku suka kamani fa yanzu idan su Daddy ya tambaye ni bansan me Zance musu ba".
Babu abinda ya zo bakin Baffa sai Mizi yasan shine Wanda zai aikata tunda Yana da yaya a makarantar su. Haka ma Mujahid Jaz ne ya zo bakin sa, a kusan tare suka ambaci sunan.
"Ohh kunsan su Kenan? Kun aikata".
Hawaye na zuba sosai a idan ta.
Baffa fita yayi bazai iya jure ganin kukan kauwar sa ba.
Mujahid kuma Kwantar ta yayi a kafadar sa yana shafa mata bayan ta ya kasa furta koda kalma Daya ce.
"Saboda ni aka kamashi, saboda ni aka dake Shi, saboda ni aka sare Shi, komai ya faru saboda kun Shiga harkar sune".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...