8

114 15 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023











*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰

*TUKUICI GA:* sweetheart😘

*SHAFI NA 8📑*

*__________📖* Yau da wuri ta shirya suka fita tare dasu Sultan suka ajje su kuka suka wuce sai da suka fara ajje sultan Sannan suka tafi wayanci lokuta haka suke.

Tana shiga ba kowa sai ita kadai ta Shiga ta zauna a can lungun ta fara bitar karatu tana cikin yi bata ankara ba kawai taga mutum a tsaye a gaban ta Dagowar da zatayi taga Malam Iliya Yana wani murmushi Yana kallan ta Bata San sanda ta doka masa harara ba ta cigaba da abinda take Zama yayi.

Yace, "Maryam ya da haka Ashe kin dawo ko ki nemi ni?"

Ita de cigaba tayi da Karatun ta duk da taji Shi amma sai ta nuna bata ji ba.

"Ya kamata ace kin saurare ni haba Maryam ina ta maki magana?"

Batare da ta kalle Shi ba, ta tsayar da karatun tana sauraran sa.

"Yawwa ko kefa, da zaki ke zuwa da wuri kamar yanzu kinga kullum sai mu dinga haduwa ko? Kinsan ina San ki sosai fiye da yarda nake San Rai na ina kaunar ki sosai so nake kawai ki aminci min naje neman auren ki, kuma kin ki ko kulani ne narasa gane wa kanki".

"Sannan kuma abin na gaba kamar de yarda na fada kike zuwa da wuri kamar ko karfe Shida ma sai mu sami lokacin magana sosai har nake maki karatu".

"Ki amsa min mana Habibti kiyi magana ko naji sanyi a Rai na tunda daga waje naji zazzakar muryan ki na karatu fa shine kawai zuciya ta ta Bani kece please kiyi magana".

Idan kujeran da take Kai ta tanka to itama ta tanka ganin an fara zuwa yasa Shi fita Yana aiyana abubu da dama a ransa, da harara ta raka shi a zuciyar ta.

Tace, "Munafiki har wani nake zuwa karfe shida uwar Ka zaka min? Wai karatu, Kama goge wa Kanka hadda nida da Ka Kara gani na na nazo yanzu sai har abada Munafiki kawai".

Tsaki taja ta cigaba da karatun ta, malamar bata zo ba sai 8:30 tana zuwa ta fada musu saukar su Nanda wata Uku bayan lokacin anyi sallah, ta kalli Siyama.

Tace, "Maryam kece de bansan  ya zakiyi ba, tunda bakiyi nisa ba dole ajin Malam Iliya zaki koma hakan zaifi tunda babu yarda za'ayi ace kinyi covering nan da wata uku".

Cikin muryan masu hankali.

Tace, "Malama Zan iya, tunda ina zuwa ta asabar da lahadi ga kuma wannan daneke zuwa harta yamma ina zuwa inaga Insha Allah zan iya basai na koma can din ba".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now