39

97 13 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

MARRIAGE IS A LIFE-LONG JOURNEY BY THAT THRIVES ON LOVE, COMMITMENT, TRUST, RESPECT, COMMUNICATION, PATIENCE, AND COMPANIONSHIP.

     HAPPY MARRIED LIFE AMINA M. SALIS (SWEETHEART).

ALLAH UBANGIJI YA BADA ZAMAN LAFIYA MAI DOREWA, ALLAH YA KAWO MANA YARA MASU ALBARKA.

       AMEEN YA ALLAH.

 

*SHAFI NA 39📑*



*__________📖* Wani irin ajiyar zuciya suka sauke lokaci guda jin kirarin da ake musu yayin da suka kusa zama statue domin mararbar kad'an ce, su suna ji sai kuma idan su ya fara ganin mutane suka fara bin mutane da kallo da sannu suka fara fitar da numfashi sannan kuma suka fara neman mutumin da yazo da su dan shi kawai suka sani sai dai babu shi babu dalilin sa.

"Kunga ku matsa musu haka suje su huta ai sun sha hanya".

"Gaskiya kam sunyi namijin k'ok'ari gashi sun had'a zumunci fatan mu Allah ya 'kara dank'on zumunci ya kuma basu zaman lafiya".

"Amin".

Jama'a suka amsa, sude kawai nasu binsu sukayi da ido, babu baka wanda ya fara maganar ta farko ne yace.

"Ku tashi kuje ku ku huta idan anjima za'a kai ku d'akin amaren ku".

"Yaushe zamu tafi?"

Mizi yaji maganar ta fito batare da yasan yayi hakan ba".

"Ai lokacin kad'an kude ku tashi".

Babu yarda suka iya dole su tashi gashi basa jin zasu iya yiwa mutumin rashin musu bare kuma wulak'anci bugu da k'ari kuma yafi Dad kwarjini, salo salo dasu suka bi bayan shi har zuwa wani d'aki ko suce bukka aka zaunar da su.

"To anan zaku huta bari nasa a kawo maku kaya da abinci sai kuyi wanka kuyi sallah kuci abinci sannan ku huta ka gado nan".

Ya fad'a yana fita bin inda yacewa gado suka bi da kallo inda suke zaune kowa d'aya d'aya suna facing junan su had'a ido sukayi suka kalli juna a karo a na farko tun zuwan su, kafin su sami bakin magana kuwa tuni anyi sallama an shigo tare da ajje komai sannan akace.

"Ruwan wanka na waje, nan baya ne kewayen".

Ya fad'a yana musu kwatance.

Daga haka suka fita daman maza ne guda biyu suka kawo musu.







☘️





A hankali ta bud'e idan ta tana addu'a mik'a tayi tare da juyowa kawai taji taci karo da mutum a bayan ta rabin jikin ta ma ya hau kan sa k'ara juyowa tayi cike da mamaki  tana kallan sa sai kuma ta girgiza kai tana murmushin mutumin da jiya yace a parlour zai kwana da ta tashi sallah ma a kusa da ita ta ganshi.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now