*°🔘°A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad @ *HijjartAbdoul.*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗
*TUKUICI GA:* sweetheart
*SHAFI NA 48📑*
*__________📖* yace, "Nace naji, daman ai kunne ke ji ba? kuma naji".
Wani irin mamaki ne ya lullub'e Hajjaty dake zaune bata san ma ta taso daga jikin kujerar ba tana kallan shi shima ita yake kallo kallo cikin ido ma kuwa idan sa bata ganin komai sai tsantsar b'acin rai yau ba damuwa take gani ba b'acin rai ne take hangowa.
"So kike nace naji to naji".
Yarda yayi maganar cikin tsawa ba Hajjaty da akayiwa ba har ta Siyama sai da ta tsorata kallan shi kawai take gashi ya k'ara damk'e hannun ta sosai ba damar kuncewa dan riko ne bana wasa ba gashi cikin b'acin rai, Zakiyya kuwa wayar dake hannun ta sai da ta fad'i k'asa jikin ta kuwa rawa ya kama yi, Hajjaty yawu ma kasa had'iye wa tayi cikin d'aga murya.
Yace, "Auren ta zanyi ba? zan aure ta tunda haka kike so amma kisani tamkar ta shigo cikin wuta ne ko wacce rana zata ke fuskantar k'una da zafi gami da rad'ad'a har sanda wutar zata mutu ranar mutuwar ta kenan, wannan alk'awari ne".
Hajjaty de kallo ya kasa k'arewa bama ita kad'ai ba kowa kallan sa yake cike da mamaki da kuma tsoro, tashi tayi da ita a hannun sa dole itama ta tashi ya kalli Zakiyya.
Yace, "Ke kuma kin yarda zaki auri k'azami? zaki auri jahili? marar tunanin? dak'ik'i? marar aikin yi? mai kwana gidan karuwai? mashayi? b'arawo? kin yarda zaki aure ne a haka?"
Wani irin hawaye ne ya zubo mata tunawa da tayi ta tab'a fad'a masa wannan kalaman daman be mantuwa? kallan ta yayi cike da wani irin kallo tare da rungumo Siyama.
Yace, "ita tayi, ta auri wanda bata san waye shi ba? a'ina yake? halin sa bata sani ba amma keda kike kin sani meyasa sanda aka ce ki aure ni kika k'i? dalilin da yasa yanzu kike ce kina son auren shine bansani ba bana kuma so naji".
"Ki yarda ayi auren za kuma ki ga abinda zai faru daga ke har ita".
Yaja hannun Siyama suka tafi ita de kawai kallan sa take ta kasa koda magana daman me zata ce? k'ifta ido ma bata san tana yi ba ya bata mamaki k'warai dagaske.
Bata san ma sun zo parlourn su har ya zaunar ta sai gani tayi kawai ya fice sannan ta maida numfashi ta fara ajiyar zuciya kai kace ita aka fad'awa maganar dan iya tsorata ta tsorata sosai.
Wayar ta ce tayi k'ara ta kalla screen d'in taga Sultan ajiyar zuciya ta sauke ta saisai ta kanta tayi kamar ba wani abu sannan ta d'aga.
"Meye zaka wani kirani ka tashi daga mayen ko da saura".
"Mtsww! dalla ba wannan".
"To inaji".
Fad'a mata abinda ya faru yayi.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...