*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 20📑*
*__________📖* Gaba Daya ji tayi ta rasa nutsuwar ta, ga wani irin faduwar gaba da taji gaban ta Yana yi a hankali ta juyo ta ganshi Yana kallan ta ya sakar mata wani killer smile Mai kwantar da hankali Shi da'alama de babu wannan faduwar gaba a tattare dashi fuskar sa normal sai wannan kwantattacan murmushin dake fuskar sa be dauke ba.
A hankali ya taka ya wuce ta ganin ya Shiga ciki yasa ta sauke ajiyar zuciya da tattaro dukkan nutsuwar ta, ta bishi can karshen baya yaje ya tsaya Yana kallan ta har ya karaso ya mata Alama da hannu da ta shiga Shiga tayi ta zauna sannan shima ya Shiga ya zauna.
Cikin sanyin muryan sa kuma can kasa yarda zata jishi.
Yace, "relax! All is well".
Daga masa kai tayi badan ta yarda ba sai dan ba yarda zatayi hakan shine kawai amsar ta Amma ita Kam har cikin zuciyar ta tana Jin tsoron Mizi.
Fito da handout din da ya Karanta jiya yayi yana kallan ta tare da sakar mata murmushi ganin Shi take kallo.
Yace, "mu fara?"
Daga masa kai kawai badan ta samu nutsuwa ba.
Mizi kuwa tsabar takaici da bakin ciki kasa magana yayi, ganin sun wuce Shi babu ko magana duk maganar da ya zo da ita ma sai yaji ta gudu ta barshi dunkule hannun sa yayi cike da bakin rai kafin ya hadiye bacin ran dake fuskar sa ya boye Shi bakin cikin ya daya taso masa, ya saka hannu a aljihu yayi ya nufi wurin su Yana wata irin tafiya irin bayani.
A Saman desk din dake gaban su ya zauna Yana kallan su tare da sakar musu shu'umin murmushi.
Yace, "Ohhh! Kuna da wayo fa, imm naci zaku Kai kara ai ashe baku Kai ba, hahaha da ace kun Kai kune a wahala dan da yanzu an rufe babin ku sai dai a tahiri".
Shiru yayi yana kallan su ganin ko kallan sa basu yi ba, yayin da gefe guda Sameer ya damke hannun ta ganin zata kalle shi gashi kuma ta tsorata hakan yasa Shi daura hannun sa a saman nata alamar Kar tayi wani motsi.
"Hakan yayi kyau, Shirun da muka muku muna san muga iya gudun ruwan Ku ne yanzu kuma mungani baku da wani zabin da ya wuce duk abinda muka muku kuyi shiru amma kusani wannan abin da Zan maki yayun ki da suka Shiga harkar ta sai sun zubar da hawaye a gaba na sai sun dandana kudar su muna nan dake".
Daga haka ya tashi zai tafi har ya juya sai kuma yajuyo daidai nan shima ya dago Kansa dan ganin sa.
Yace, "Bansan Ka ba, amma tunda Ka shigo fadan fine".
Ya karashe da daga kafadar sa alamar shikenan, da kallo suka bishi har ya fita daga hall din, ajiyar zuciya ta sauke Wanda shima sai da yaji.
Yace, "Ehhmm ashe wata matsoraciya ce to wai de".
Ta cikin Nikaf din ta, ta balla masa harara.
Tace, "wace matsoraciyar?"
"Wata nace fa, idan kuma kin sake tankawa to kece matsoraciyar bani ba".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...