*°🔘°A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad @ *HijjartAbdoul.*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗
*TUKUICI GA:* sweetheart
*SHAFI NA 43📑*
*__________📖* "Mustapha kasan kuwa me nake magana a kai?"
"Nima de Yaya baka san me nake maganar ba akai".
Shafa kan sa Muzzaffar yayi yana sakin wata irin ajiyar zuciya gaban sa na fad'uwa sosai ya kasa tan tance abinda ya gani.
Mizi yace, "To wai kai Yaya me ka gani?"
"Shiga ka gani".
Ya bashi ya amsa, shiga yayi d'akin yana shiga ya fito.
"Nima irin shine ai, mekenan?"
"Kawai kazo muje mu cire wannan abin, mu bayar shi can d'akin bak'i mu dawo da wannan nan".
"Haka za'ayi, ina zamuyi wani ta zama da wannan shirmen a d'aki".
"Baku isa ba".
Sukaji muryan Daddy ya fad'a, cak suka tsaya ganin sa fuskar nan a d'aure take tamau babu ko d'igon annuri a ciki ta gashi yasha babbar riga ta wani k'ara masa kwarjini tsoro tsoro sukayi suna kallan sa.
"Wannan auren da kuka ga gudarwa kusani duk inda kukayi suna biye da kune, na fad'a maku abinda baku sani ba sun riga ku zuwa yarda kuka jeran su na kaya haka zaku zauna".
Juyawa yayi ya tafi har yayi taku uku zuwa na hud'u ya tsaya tare da juyowa.
"Duk wanda na k'ara gani ya taka koda k'ofar parlourn nan hmmm... Bansan me zan masa, Allah ne kad'ai ya sani".
Ya fad'a yana tafiya abinsa yana yin wurin Ummi.
Kallan juna sukayi kafin sukayi k'wafa suka shiga.
Muzzaffar na shiga ya hango ta can cikin gadan ta, gaba d'aya d'akin ya koma fasalin kalar abinda ya baro a k'auye banbanci wannan akwai kayan more rayuwa shine kawai banbancin su dashi amma komai iri d'aya ne abin shikam yayi matak'ar bashi mamaki da alajabi taya za'ayi ace sun riga su zuwa sai kace aljanu? wata zuciyar ta bashi amsa da Hainasu nada su ai ba mamaki ita ce wani irin tsoron yarinyar ne ya d'arsu a zuciyar shi sannan yayi hanyar toilet yayi wanka ya fito ya bud'e mitsitsin wardrobe d'in da yafi ta tsaye ya d'auki kayan sa yasa ya feshe jikin sa da turare sannan ya fita parlour yaje ya zauna yasha kunu jiran dawowar Mom kawai yake ya sauke mata kwandan rashin kunya.
Mizi kuwa yana shiga ya ganta da da farko do shigo sam be ganta ba sai yanzu ya ganta a wurin window tana sak'ar hula tana rera wak'ar ta.
"Ke!, Ke!, Ke dan uwarki kina jin ana kiran sunan ki?"
"Da ina k'arama muna zuwa wata makaranta an tab'a koya mana a, be, ci de, bansani ba ko hi kake karantawa hine kake K, to daga ita ai sai L idan ban manta ba haka ne?"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...