*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 21📑*
*__________📖* wata daya suka dauka suna exam, a cikin wata d'ayan nan wata irin shakuwa ce ta shiga tsakanin su ta wuce misali yasan halin ta kamar yarda 'yan gidan su suka sani, duk zaman da suke bata ta'ba tambayar sa 'yan gidan su ba kuma shi be fada mata ba, haka ma duk iya surutun ta a gida bata taba basu labarin sa ba banda sunan da Sameer babu abinda tasani game dashi.
Yau sukayi last paper suna zaune inda suka saba zama yau kam da mutane da yawa kowa na sallama da Wanda yake kusa dashi wasu yau zasu tafi wasu kuma gobe wasu ma Basu gama exam din ba.
"Wai baza ka dena kallo na ba?"
"Banasan hutun nan".
Juyowa tayi ta kalleshi ta kawar da kanta duk da itama can kasan zuciyar ta bata son hutun bata nuna masa ba.
Tace, "amma naga de zamu ke waya ba?"
"Waya kuma?"
"Uhm hum".
"Bani numbern ki Zan Kira ki".
Bashi tayi.
Tace, "bari na tafi yau ya Mujahid ba zuwa zaiyi ba".
"Ki bari sai anjima please".
"A,a yanzu zan tafi".
"Meyasa?"
"Kowa yasan yau zan gama exam dina kuma da wuri zan dawo bana so Mama tayi min fada kuma yau Friday Daddy da wuri yake dawowa".
Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi.
Yace, "to muje na rakaki".
Itama tashi tayi ta rataya jakar ta suka tafi suna yi suna hira har suka je bakin gate ta samu napep ta hau ta tafi shima ta samu wani ya hau a yarda yake ji idan be sha giya ba bazai ji dadi ba ko kadan hakan yasa Shi wucewa club acan ya biya Mai napep kudin sa sauran kudin kuma ya siya giya har gwalba uku shi Kenan kudin da Daada ya bashi ya karar shi.
☘️
Tana koma wa ta iske ba kowa a gidan sai Sultan har yayi shirin masallaci.
Tace, "Ina suke 'yan gidan?"
Kallan ta yayi ya dauke Kai.
"Kasan Allah Sultan Ka kiyaye ni ina maka Magana kana wani yimin gatsine ko? harda murguda min baki".
"Kaiii! Kike Jin tsoron Allah Siyama yaushe nayi maki gatsine? Ke wai idan bakiyi k'ari ba a zancen ki bakya taba Jin dadi?"
Zanja channel tayi.
Tace, "hala yau guduwa kayi daga makaranta ko?"
"Guduwa mukayi ba'a tashi ba".
"Inyeeee sannu tou".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...