💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝
Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023Da wuri Mama ta tashi duk da ya kasance weekend Amma tana da morning, kuma daga wurin aikin zasu wuce Gombe, Siyama ta tarar a parlour tana kallo.
Mama tace ''Siyama tashi ki gyara parlour nan da kallan da kika zauna kina yi da tuni kin gyara".
Turo baki tayi gaba, tana cigaba da kallan ta.
tace ''Mama ina kwana".
Tsaki mama tayi ta wuce kitchen itama tashi tayi ta biyo mama kitchen din ta zauna akan table.
tace ''Mama daman yunwa nake ji tun dazo ".
Ta fada tana ya mutse fuska tare da taba cikin ta ko kallan ta mama bata yi ba, ta fara aikin ta dankali ta debo da yawa ta ajje a kusa da ita ta dauko filler da wuka ta debo ruwa ta ajje, siyama na kallan ta tana cigaba da magana.
Mama tace ''oya fere min ki soya".
Kallan Mama tayi zata yi magana mama ta wurga mata harara, tuni ta dauka ta fara fere wa can,
tace ''Mama".
Shiru Mama tayi bata amsa ba, ta kuma, cewa ''Mama".
"Mama de".
"Mama fa".
"Mama ina magana".
"Mtsww meye kike Kira na?"
Kumbura baki tayi ta cuno shi,
tace ''daman tambaya zanyi, nace du za'a fere ne dankali? Kinga baya na har ya dan fara ciwo-ciwo kin san dana fito banga zuma ba, nace ko ta Kare ne?"Mama tace ''kiyi aikin da nasaki kafin ranki ya baci, kin dawo zaki fara masifar shan zuman naki".
"Mama fa..."
"Kim rufe min baki kin yi abinda zaki yi ko sai na fasa maki wannan bakin da kike zunbora wa".
Daure fuska tayi ta fara gunguni.
"Yau zamu tafi Gombe da Abban ku da Anty kwana zamu yi a can bana san fitina ki tabbata kuma kinje Islamiyya da ta safe da ta yamma ki tabbas kinje,idan kinje Zan sani idan baki je ba ma zan sani ni dake ne".
"Mama kinsan bana san wannan islamiyyar duka suke nikuma da girma na yanzu kawai a kafa duka na, haba wa mama ai be dace ba".
"Haka ne kam beda ce ba fa ashe to shikenan kiyi ta Zama".
Tana firan dankalin ta fara waka, ganin Mama taki cewa komai.
tace "Mama yaushe wannan mai aikin zata zo ne".
"Yau baza ta zo ba haka gobe".
"Ke kika ce mata Kar tazo?"
"Kin san zan aikata ai".
Cigaba da wakar ta tayi tana fare wa, har mama ta Gama abinda zata yi ta fita tana aikin fere wa, ganin Mama ta fita kuma saura kadan ta gama sauko wa tayi ta mayar da sauran cikin store sannan ta fara yanka wa ta yanka kadan ta daura Mai sannan tsame wanda ta yanka da mai yayi zafi ta zuba Shi, kafin ta gama yanka wa, wancan ya kusa soyuwa.
"Daman hakan nayi da ina fere wa da tuni na gama".
Saida ta kwashe ta zuba wani ta fito parlour, agogo ta kalla taga lokaci ko 8 ma bata karasa ba, tade kusa, parlour ta share tana yi tana leka kitchen ahaka ta gama gyaran da suyan dankalin, shima kitchen din gyara wa tayi tsab ta wanke dan kwanikan da ta gani sannan ta kwashe kayan da Mama ta hada ta kai tsakiyar parlour ta ajje, komai ta kawo ta ajje, ta zauna ta deba taci ta sha tea ta tashi ta koma ta cigaba da kallan ta.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...