*°🔘°A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad @ *HijjartAbdoul.*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗
*TUKUICI GA:* sweetheart
*SHAFI NA 42📑*
*__________📖* Basu suka isa ba sai 3:30am iya gajiya sun gaji saboda tsaye tsaye ran kam ya gama b'aci a haka de suka k'araso suna k'arasowa aka ajje kowa sannan suka ce da drivern ya kai su gida zasu biya bashi wani abu suna kwatan ta masa kuwa ya kaisu ya dire su knocking sukayi mai gadi ya taso yana lek'awa ta hasken dake zagaye da gidan ciki da waje shine ya bashi damar ganin su bud'e musu yayi yana musu sannu da zuwa.
Yace, "Yallab'ai nace amm sai dai kuje wurin bak'i dan a bud'e yake kasan yanzu dare ne".
Ya fad'a yana wani irin rissinar da kai cike da ladabi.
Muzzaffar yace, "Dad yana nan?"
"Ehh yana nan, jiya ya dawo daga tafiya ma ai".
"Muje ka bud'e mana".
Suna binsa a baya kuwa ya bud'e musu b'arin bak'in dake gate na farko kafin a shiga cikin gidan ta wani gate d'in suka shiga kowa d'aki d'aya ya nufa yayi wanka da ruwan zafin da suka ji kamar sunyi shekara basuyi ba, sosai suka dirje jikin su sannan suka fito ba kaya dole de nasu zasu mayar sai kawai suka sa kayan ciki abinsu tare da hayewa gado suka rufa da bargo sai bacci.
☘️
Washegari da safe tana tashi ta had'a masa breakfast sannan tayi masa abincin tafiya kafin ya dawo, gashi wani irn ciwo jikin ta ke mata haka de ta daure tayi abinda zatayi yau ma batayi shara ba bare mopping gani take gidan ta tas yake hakan yasa batayi ba kuma a gajiye take, ganin be dawo ba yasa ta zuwa ta gyara d'aki tare da wanke bayi tayi wanka ta shirya sannan ta fito lokacin shida da mintuna yayi taga saurin ta sosai main parlour ta nufa tana tunanin ina ne b'arin Hajjaty? Kallan k'ofofin dake wurin tayi sannan ta nufi wata k'ofa ko za'a dace aikuwa wani k'aramin parlour ne mai masifar kyau da tsari kamar parlourn yara d'an cib dashi ya mata kyau sosai sai kuma k'ofa biyu da taga gani a hankali ta shiga d'ayar babu kowa a ciki hakan ya bata damar duba abinda zata duba sai dai kuma bata gani ba tayi duba iya duba bata gani ba dak'yar ta gani kawai sunan sa tagani Sameer ta kwaso duk abinda take tunanin nashi ne na makaranta sannan ta mayar ta fito tana sauke ajiyar zuciya sad'af ta fice batare da ta ko juyo ba.
yana parlour yana rik'e da mug a tsaye yana safa da marwa da'alama ita yake jira tana shigowa.
Yace, "ina kika je?"
Abinda ta b'oye a bayan ta ta fito dashi sannan ta nuna masa, hannun yabi da kallo sannan ya kalle ta.
Yace, "kede ko? gashi duk kinbi kinsha wahala".
Ya fad'a lokaci guda yana ajje abin hannun sa tare da fara goge mata gumin daya kwanta a goshin ta.
"Idan ta ganki fa?"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...