60

101 10 0
                                    

🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•*

*SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''

*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

'''The starting point of all achievement is desire. Keep this constantly in mind. Weak desire brings weak results, just as a small amount of fire makes a small amount of heat.
'''

*Prophet Muhammad (SWA) Said: "whoever recite SURAH YASEEN once, ALLAH Will record the reward of reciting the QUR'AN TEN TIMES".*

_Tirmidhi 2812/A_

*SHAFI NA 60📑*

*__________📖* Tana zuwa bata zame ko ina ba sai d'akin ta, daman Abbas ne ya kawo ta ba zuwa yake ba bare ace sun wani saba da mutanen gidan, yarinyar ta ajje sannan tayi part d'in Hainasu tana zuwa tagan ta tana had'a kaya tana kuka ga yarinyar ta nan da'alama d'auko ta tayi daga makaranta tana zaune tana shan sweet abin ta.

"Anty Hainasu? lafiya?"

Cike da mamaki take kallan ta kafin ta k'araso kusa da ita ta tab'a ta.

Tace, "wai meke faruwa ne?"

"Ummita me ya samu Maman ki?"

"Nima bansani ba, zuwa tayi kawai ta d'auko a makaranta ta dawo dani tace Kebbi zamu tafi ganin tana kuka shine nima na fara kukan tace na dena ta bani alawa amma ita bata dena ba kice ta dena ko nima nayi kuka".

A lokacin ne ya zuge ajakar ta, sannan ta tada ita tsaye ta d'auki ta wata ta kai parlour ta dawo ta d'auki wata ita de Ummi kallan ikon Allah kawai takeyi, har ta kai ta k'arshe ta dawo taja hannun Ummita zasu fita daga d'akin da kuma key a hannun ta alamar zata rufe yasa Ummi saurin rik'e hannun ta tasa ta bayan ta.

Tace, "Kinsan bazan barki ki tafi ba? sai kin fad'a min abinda yasa ki kuka? meye ma haka? baki tashi tafiya ba sai yanzu?"

Goge hawayen ta tayi tana kallan ta da idan ta da yayi ja.

Tace, "kina san sani? kina san dalili?"

"Bana san sani na tambaye ki?"

Hawaye ne ya zubo tasa hannu ta share sannan ta zaga yo ta d'auki 'yar ta.

Tace, "zaki iya biyo ni?"

"Zuwa ina?"

"Biyo ni".

Bata jira cewar ta ba tayi gaba, binta Ummi ta fara yi a baya kamar jela har suka iso parlour a zaune suka tadda Mom kana gani zaka san wani tunanin ta tafi.

A gaban ta suka tsaya ta kalli Ummi hawaye na zuba a idan ta sosai.

Tace, "Tambaye ta, me mijin ki ya musu suka shirya kashe shi garin haka sai Allah yayi harda nawa mijin aka tafi".

K'ara goge hawayen ta tayi, tana kallan Ummi ganin irin kallan me kike cewa take mata baki a bud'e tana so tayi magana amma zuciyar ta tokare ta.

Tace, "Meye kike kallo na haka? kallan ta zakiyi ki tambaye ta dalilin yin haka shi nake so naji bawai ki tsaya kina kallo na haka ba".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now