56

92 11 0
                                    

🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•*

*SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''

*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 56📑*

*__________📖* Akan lalle lalle baza su yi sallah ba sai sunje sabida be san rasa jana'iza ada besan adadin yawan ladan ba amma a yanzu ya sani duk inda aka yi mutuwa zaka same shi koda be san mutum ba indai har ya ga za'a kai gawa to dashi ake zuwa koda kuwa be sallaci sallahn ba.

Tun daga nesa yake hango babu kowa a wurin titi fental dashi sai tsirarin mutane na wucewa da 'yan islamiyya suma daya daya, ita de bata yarda sun had'a ido ba sai ma k'ara goge idan ta da take har suka sauk'a a daidai saitin gate d'in ya biya mai adaidai ta suka shiga da Baba suka fara cin karo zaman sa kenan ya dawo daga masallaci.

Yace, "Lalala yau uwar d'aki na ce kenan tazo mana".

"Baba ina wuni".

"Lafiya qalau ya kike?"

Sunkuyar da kai tayi tana amsawa.

Sameer yace, "Baba ina wuni?"

Ya fad'a yana durk'usawa ganin yarda tayi.

"Lafiya qalau".

"Ya akaji da hakurin mu".

Da yake su manya sun saba duk wayancin gaisuwar sai sunyi maganar hakuri ba dan mutuwa ba sai dan zaman takewar rayuwar ta yau da kullum sai a hankali.

Yace, "Alhamdulilla ai daman kasan sai hakuri, fatan mu a kullum Allah ya kara mana hakuri da juriya".

"Amin".

Sannan suka tashi dan shiga ciki kallan ta yayi.

Yace, "ya bana ganin mutane?"

"Ko yanzu nan akayi ba?"

"Ohh haka ne fa".

Sai kuma ya tuna sanda ya fara zuwa gidan da kuma sanda ya kawo ta da suka gudo da zuwan sa na k'arshe wanda yake ganin yayi sallama da farin ciki, yana cikin tunanin suka k'araso, a balcony ta tsaya tana kallan shi.

Yace, "muje mana".

"Ina tsoron shiga ne fa".

"Hala kinyi wani laifi ko?"

Had'iye miyau tayi sannan ta tura k'ofar tare da cire takalmin ta tashiga shima bin bayan ta yayi tana shiga ta manta da wata sallama kawai tayi kan Mama a guje tana fasa wani uban ihun muryan sai da ta tsorata Mama gashi ta wani k'amk'ame ta.

Mujahid da Baffa fitowa sukayi ganin meke faruwa kamar ihun ta suka ganta a tare suka saki tsaki kuma fa sunji dad'in ganin ta sosai sai suka wayenci da zuwa wurin mijin ta ganin ya tsaya yana kallan ikon Allah.

Mama tace, "Ke dalla d'aga ni bansan shashancin meye haka d'in?"

Turb'une fuska tayi ta zame ta zauna a gefen ta ta turo baki.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now