32

94 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*

*1442H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

*SHAFI NA 32📑*

*__________📖* "Ya Mujahid gaskiya nikam nagaji mu tafi anan wurin".

"Uwar waye yace azo?"

"Ya Baffa Kode daman kunyi waya ne da ita? zaku had'u anan?"

"Ranki zai b'aci".

Turo baki tayi tana cigaba da shan ice cream duk ta b'ata bakin nata.

Mujahid yace, "da wani k'atan bakin ki a wurin kamar na saniya".

Yatsine fuska tayi zatayi kuka jin abinda yace mata kace mata komai amma banda yiwa bakin ta ba'a tana san bakin ta, dagowar da zatayi taga su Mizi na iyowa wurin su had'a idan da sukayi dashi ya wani kashe mata ido gashi ta hango Yayan nashi shima yana tahowa surrender tayi ta kasa d'auke idan ta daga garesu bakin ta ya kasa furta koda kalma d'aya ce, Mujahid da Baffa a tare suka juyo ganin yarda take motsi da bakin kuma ta tsorata ganin su Mizi yasa su b'ata, Baffa ya juyo yana kallan ta gaba d'aya a tsorace take, suna k'arasowa ko magana basuyi ba suka sami kujera suka zauna sai ga Yayan nan shima be zauna ba yaje ta wurin tsakanin Baffa da ita ya d'aura k'afa a akan kujera yana kallan ta, ita kuwa sai kiftawa ido take ta kasa motsi.

Hannu yasa ya dan kwali ice cream din dake bakin ya lasa.

Yace, "Woww, so sweet".

Zai k'ara sa hannu Mujahid ya rik'e hannun yana masa kallan da ya kasa gane na meye.

"Bata da laifi dan haka kada ka kuskura ka sako ta a cikin fad'a mu".

Baffa yace, "Kasan bazasu sani ba tunda ba'a san abinda yake dai-dai ba".

Mizi yace, "Mu kake fad'awa wannan maganar?"

"Tambaya na kake na baka amsa? ko kuma de so kake na tabbatar da abinda na fad'a?"

Muzzaffar yace, "uban ku waye a fad'in garin nan da kuke da wannan tak'amar muke juyawa duk wani d'am iska a fad'in garin nan amma ku taurin kan ku yayi yawa bakwa ganewa".

"Zamu ganar dasu da yaren da zasu gane".

Mujahid ya sai a lokacin ya saki hannun sa ya tashi tsaye yana karkad'e hannun.

Yace, "Kuke juya duk wani d'an iska, munce muku mu 'yan iska ne? wanda kuke juyawa kuke
masu abinda kuka ga dama gani sukayi zasu iya".

"Dan uwarka ni kake fad'a wa wannan maganar".

Ya fad'a yana cakumar rigar sa.

"Hey! Relax Man".

Mujahid ya fad'a yana cire hannun sa dake wuyan sa yana kuma gyara masa kwalar rigar sa.

Yace, "Yanzu sai an tab'oka kace kasan muhimman ci uwa, idan aka ambace ta kuma kake tada jijiyar wuya ashe ba'asan darajar ta".

Baffa yace, "Taya za'ayi su sani wai Ya Mujahid? har aka bud'i baki aka zage ta".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now