*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 38📑*
*__________📖* "Ke baki san da cewa lusarin miji kika aura ba ko? da bazai iya siyo maki kayan miya ba sai anje an min sata ko?"
A sukwane Siyama ta d'ago da kan ta tana kallan ta, itama kallan ta tayi.
Tace, "Ehh! sata k'arya nayi? basatar yayi ba kike wani kallo wai ke mai miji".
Sunkuyawar da kan ta tayi tana jin wani irin takaici da bak'in ciki yana taso mata.
"Kai sata kayi ko ba sata kayi ba".
Batare da ya d'ago ba.
Yace, "d'auka nayi".
Shiru tayi tana kallan sa, na wani seconds.
Tace, "sata kayi ko a'a?"
"Na d'auka nayi".
"Dan uwar ina magana kana magana?"
Shiru yayi be kuma san be zai ce mata ba.
"To ke! kisani wannan lusarin mijin ki b'arawo tunda gashi nan kin gani daga zuwan ki, idan bakiyi taka tsantsan ba kema kya bi sahu daman ance abokin b'arawo, b'arawo ne daga nan sai ku zama thiefs family shikenan za kuma ku aikata".
Idan zuciyar Siyama tayi dubu ta b'aci daman ace irin zuciyar 'yan gidan su ce da ita wacce zata iya tanka mata da yanzu tayi ta k'are kulle idan ta tayi tana jin zafin da bata tab'a jin ba musamman idan ta kira shi da lusari.
"Ohh ashe fa Baban ki yana da kud'i tunda har zai iya tura 'yar sa da kayan garan da ba'a tab'a yi ba ban kuma tab'a jin labari ba wai ku kuna min kuna da kud'i ko?"
Shide idan sa a k'asa be d'ago ya kalle ta ba bare yasan kallan su take yana kora musu jawabi tunawa yayi da sun d'aura miya zata iya konewa kuma tunda daman sun kusa kammalawa, hannun data rik'e cikin d'aya wanda tuni hawaye ya fara zuba yana d'iga a hannun, hannun yabi da kallo sannan yasa hannun sa ya kama nata.
"Daga yanzu baku ba yin hanyar kitchen d'ina ke ubanki badashi aka gina ba kai kuma Uwar ka ko asi bata barmaka ba na gado bare..."
Gani tayi ya d'aga ta ya kuma kama hannun ta sun tafi ko juyowa ma basuyi ba, wani irin tarin takaici taji yana taruwar mata a zuciya.
"Mu zuba mu gani".
Ta fad'a tana k'wafa tare da maida kallan ta ga tv.
Suna shiga ta warce hannun ta tare da wullar da mayafin ta ta zauna tana goge hawayen ta tare da maka masa wata irin harara idan ta yayi jajur, jikin sa ne yayi wani irin mugun sanyi a sanyaye yazo kusa da ita ya zauna ita kuma ta had'a hannun ta ta d'aura hab'ar ta akai idan ta yayi ja wanda yake nuna taji zafin abin, duk kukan da zatayi ba sosai idan ta yake ja ba.
"Kiyi hakuri, bahaka bane".
Ya fad'a tare da d'aura hannun sa a kafad'ar ta.
"Wanne aiki kake?"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...