40

105 13 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 40📑*

*__________📖* A hankali ta fara bud'e idan ta dake cike da bacci da gajiya gami da wani irin nauyi da suke mata ga wani irin sarawa da taji kan ta yayi, ta ware su a fuskar sa da take da facing nata fuskar sa tayi wani irin fresh da yana bacci yana murmushi, hannun ta tasa ta fara shafar fuskar sa itama tana murmushin a hankali abinda ya faru d'azu ya fad'o mata sai kuma ta dena wani irin kunyar shi ce ta taji rufe ta lokaci guda kawai ta kifa kan ta a k'irgin sa tana murmushin itama, jitayi ya rungume ta murya can k'asa k'asa.

Yace, "Garrulous da kunya? second time in history".

Dukda baya ganin ta amma yasan ta turo baki, murmushi yayi ya k'ara k'asa da kan sa sai tin kunnan ta.

Yace, "ankusa magrib".

Tashi taje yi kome ta tuna sai kuma ta kwanta ta juya baya, murmushi kawai yayi ya tashi yaje yayi alwala ya dawo.

Yace, "ki tashi kije kiyi alwalar tou".

K'ok'arin tashi tayi ta sauko, zuwa yayi ya taimaka mata ta shiga bayin tayi alwala ta fito yaja su zuwa sallah shide koda ya idar sai tsincin kan sa da yi mata addu'a kamar yarda yayi d'azu be tab'a koda yiwa Mahaifiyar sa addu'a ba bare kuma shi kan sa amma sai gashi yana ruk'ar Allah ya kare masa ita yasa mata albarka ya kuma barsu tare sosai yayi mata addu'a fiye da ta d'azu da yayis sallah.

Ita de jingina tayi da gado ta lumshe idan ta tana jan Azkhar a zuciyar ta har ta gaba bata bud'e idan ta ba bare taga me yake yi, sai da ya gama ya juyo yana kallan ta sai kuma ya matso shima ya jingina a gadan tare da janyo ta jikin sa sosai ya mata side hug, ajiyar zuciya ta sauk'e murya can k'asa k'asa.

Tace, "Baka iya komai ba?"

Shima yarda tayi maganar ta mayar ta.

"Kamar me?"

"I mean addu'a ko wani abun..."

Shiru tayi dan bata san me zata ce ba, bata san taya zata masa bayani ya gane ba hakan yasa ta jin kunya ta maida kan ta kafad'ar sa ta lumshe ido.

"Kinyi shiru".

"Kaima ai shirun kayi".

'dago da kanta tayi tana kallan sa shima kallan ta yayi.

Tace, "duk abinda nace kayi zakayi?"

"Zanyi".

"Ka tabbata?"

"Na tabbata".

"Bakace Insha Allah ba".

"Insha Allah zanyi".

"Ya kamata ka shiga makarantar da ake yiwa maza a masallaci ko ba'ayi anan unguwar?"

"Bansani ba, sai dai na tambaya".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now