*°🔘°A RAYUWAR MU °🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗
*TUKUICI GA:* sweetheart
*SHAFI NA 41📑*
*__________📖* "wai shi gida nan ba kowane sai rafka sallama nake babu wanda ya amsa, kodan babban gidan ne oho?"
Ta k'ara yin gaba sannan ta rafka wata sallamar wacce ta ci uwar wanda take a karo na ba adadi.
Hajjaty na zaune tana kallan ta tun sallamar farko take kallan ta har ta shigo tsakiyar parlourn tana neman ta wuce kitchen.
"Assalamu Alaikum Siyama Maryama".
Hajjo ta fad'a tana k'ara kiran Siyama.
Hajjaty tace, "Lafiya?"
Juyowa Hajjo tayi sukayi ido biyu da ita wato kena tana jin ta tun d'azu tana d'aga mak'oshi tana sallama amma tashere aikuwa ta d'auke irin banganki d'in nan ba ta juya.
Tace, "Siyama, Maryama wai kina ina ne?"
Da wani irin gudu Siyama ta fito dake kitchen gaba d'aya k'amshin kifi take da ta fara soyawa, haka ta rungume Hajjo itama Hajjo ta rungume ta sai suka saki ihu har Hajjo.
Hajjo tace, "Ke tsaya na ganki?"
"Hajjo kin ganni, amma kwana zakiyi ko?"
"Ke waya ce maki wani na kwana min a gida? har yaci arzik'i na? yarda ta zo haka zata koma koda garin ta da nisa ne".
Hajjo sakar baki tayi tana kallan Hajjaty dake zaune tana bayani amma tsabar masifa muryan ta rai kamar a wurin su take k'wafa tayi a zuciyar ta ta basar tare da d'auko wayar ta ta danna kira, ita de Siyama na tsaye sai kuma tayi kitchen da gudu tunawa da tayi ta d'aura abu.
"Hello, Hajjaju nace zaki zo goben?"
"Yawwa Alhamdulilla sai kizo ma kiga gidan jikar taki Siyama tunda de yaran nan baso suke muyi zumunci kizo kawai muyi wata d'aya a gidan kinsan gidan ta kamar na mu, mun iya cin arzik'i haka za'ayi ai yawwa sai kinzo".
Ta kashe wayar, ko kallan Hajjaty batayi ba tayi hanyar kitchen d'in da taga tayi zama tayi a kujeran tsugunno tana kallan Siyama dake kwashe kifi.
Tace, "ina masu aikin?"
"Sun tafi shine nake yi".
"Duk uban kifin nan".
"Na d'iba mana na kuma rage wani wannan yanzu soyawa zanyi sai na dafa wani sai kuma nayi danbu da wani".
"To yayi kyau, amma zan koya maki yarda ake girki yarda gobe baza'a saki ba".
Murmushi kawai Siyama tayi dan itama tasan wanne irin abinci zatayi jira kawai take ta kwashe nasu taga yarda ake gyara.
Hajjo tace, "ke yanzu kina zaune da irin wannan uwar mijin?"
Dariya tayi.
Tace, "Hajjo Kakar sa ce fa".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...