💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023"Lalala Daddy kaga babu wuri duk sun cike wurin, da Naga basu Duka suke biyo Ka ba, shine yau dan tsegumi har da biyo Ka su Dukan su"
Mama ta juyo tace'' baza Ku bige ta ba? Suwaye masu tsegumin? Marar kunya, waye sa'an ki anan"
Cuno baki tayi taci gaba da yi, sannan Anty ta fito,
tace'' Mai hali baya fasawa,Shiga ni "Shiga tayi aka marma matsa ta zauna sannan Anty itama ta Shiga suka kama hanya.
Shiru Motar tayi babu Mai gama, sai da gama kallan kowa taga duk sunyi shiru waya kuma babu network bare a danna,
tace'' Yaya waye ya mutu"
Daddy yace'' mutuwa kuma kauwa ta"
Tace'' Gani nayi duk sunyi shiru,kowa yayi jigum kamar mutuwa anyi mutuwa shiyasa na tambaya"
Sultan yace'' Daddy kawai neman magana ne irin nata"
Manga reshi tayi daman a kusa d ita yake tace'' wace me neman maganar?"
Yace'' Mama kiga ta bigeni?"
Mama tace'' Siyama, ki kiyaye ni, daga zuwan ki baza ki fara sani magana ba, na fada maki"
Mujahid yace'' tattaka yarinya zan yi,gwara ma mu baga maki warning tun a mota"
Anty tace'' kwarai dan baza kizo ki hanani bacci ba"
Baffa yace'' da wannan baccin safe ba, tattaka kan yarinya zanyi "
Sultan yace'' wallahi nima karya wata zanyi idan ta dame ni"
Mama tace'' kinde ji ko? Tam"
Shashshekar kuka ta fara, Kai kace gaske ne, tace'' daman nasani kun tsane ni bakwa Sona, Allah zai saka min, Yaya Duka na sukayi kuma,kuma,kuma kuma,harda sultan shida yake kani na"
Tsayawa Daddy yayi yace'' Bana San shirme,naza ci ai iya fada kuke Mata ashe harda duka,don cin zali dukan ma marar Kara?"
Anty tace'' Daddy kayi hakuri"
Kwafa yayi ya tada motar, ta cigaba da tafiya,
yace'' kauwa ta kiyi hakuri kinji, rabu dasu tsabar cin zali ne, amma fa kema kar kiyi abinda basa so kinji kauwata?"Murmushi tayi tace'' yawwa Daddy na,kuma yaya na,Mai so na"
Mama tsabar takaici shiru tayi, bata iya magana ba,
Tace'' Yaya na a Sa mana wakar shata Mai guda Darin nan"
Kunna wa yayi, sai gashi rai rai ta bi bata missing koda kalma daya, haushi da takaici ne ya ishe su,
Mama tace'' zaki min shiru ko sai na bige ki a gun, da karatu yanzu zaki kanki na ciwo ya mai aljnu, amma da yake waka ce kin iya"
Hannu tasa ta kashe, tace'' Yaya ko, yau da safe aka yi mana wa'azi a makaranta, aka ce idan munje gida muke taya Iyayen mu aiki, musamman da safe kar mu kwanta baccin safe, kasan kuma me aka kuma cewa?"
Girgiza Kan sa yayi yace'' a'a fada min"
" Ca aka ce baccin safe asara ne, duk masu baccin safe asararru ne, haka aka ce,ai yaya ko, naji wa'azi nan"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...