💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝
Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023*°🔘° A RAYUWA MU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰
*TUKUICI GA:* sweetheart😘
*SHAFI NA 6📑*
*__________📖* Be dago Kai ya kalle ta dan Shi gaskiya ya fada mata besan inda ya kwana ba bema san unguwar ba bare ya fada mata ga abu daya ya sani shine numbern gidan kuma bazai iya kai kansa gidan ba.
"Wonders! Kai yanzu har kayi girman da Zaka je gidan karuwa Ka kwana? No wonder kace Baka sani ba, ina da Zaka sani Ya Allah?"
Shiru yayi yana ji besan bezai ce mata kuma ta yarda dashi.
"Ina hauka shiyasa bazaka Bude Baki kamin magana ba".
Sai da ya bada tazarar mintuna a tsakanin.
yace, "I told you".
Itama shiru tayi tare da batar tazarar mintocin da ta bata amsa.
"Idan fadawa Mahaifin Ka".
Yana nan zaune sai ga wata Mata nan ta fito tare da Zama a kujerun parlourn ta kalli shi dake zaune be dago ya kalle ta ba dukda yasan wacece.
"Sameer yanzu abinda kake yi kana yiwa kanka adalci? Ace Ka fita sai yanzu zaka dawo? Rabon Ka da gidan nan fa tun jiya da safe sai yanzu kusan karfe Daya na rana haba".
Be bata magana kamar yarda tayi tunanin ba yi Mata zai yi ba.
"Yanzu kowa laifi na zai gani na koyawa nawa tar..."
"A gani, nace aga laifin naki sai me? Kin min shiru ko kuwa. Kar Allah yasa ya dena ya cigaba tun da yanzu ya fara kwana a gidan karuwa gaba kuma sai komawa a fara zaman daduro".
"Subhanallah! Habba Hajjaty ya kike masa wannan fata haka".
"Yaushe na fara magana kina magana?"
"Nace yaushe na fara magana kina magana? Ke! Hauwa kin San de dace auro ki nasa ayi zan kuma sawa..."
Tashin da taga yayi yasa tayi shiru bata karasa magana ba ta bishi da ido har ya shiga wata kofa Mai alamar C ya Shiga wata kofa ga dukkan alamu dakin sa ne.
Baki bude take kallan sa ta jinjina Kai tare da Dora kafa Daya Kan Daya ana jijjaga ta ta lumshe Ido ta fada kogin tunanin yarda zata yi da wannan yaran.
"Hajjaty kiyi hakuri".
Ganin tayi shiru yasa ta tashi ta koma inda ta fito wannan Mata akwai mulkin bala'i.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...