4

153 20 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023









Duk wani taku daya da take yi tare yake tafiya da bugun zuciyar ta sai taji kamar ta koma amma kuma ihun sa na taba zuciyar ta babu dadi take ji sosai, sai da tazo dai-dai wurin su ta sai saita kanta, cikin sanyi muryan.

Tace, "Dan Allah bayin Allah me yayi muku kuke dukan sa?"

Tsaya wa suka yi da dukan nashi wani.
yace, "ke yarinya yi tafiyar ki Kawai wannan da kike ganin Shi barawo".

Wani yace, "kudin mu ya sata kuma yaki ya bayar shine muke dukan sa".

Daure wa tayi tace, "kuma kun tabba shine ya dauki kudin? Duba da irin dukan da kuka masa babu Wanda zaku yiwa wannan dukan be Baku kudin Ku ba".

"Ke yarinya shine ya dauka dan mun tafi sallah kuma mun rufe shagon mu, muka zo muka gan shi a bude Shikuma a zaune yana Shan giya alamar Shi ya dauka Kenan, gayu muci gaba da dadda mas kawai".

Numfashi taja ta ajje Jin zuciyar ta ta fara dawo wa normal. Ganin zasu ci gaba da dukan Shi tayi sauri.
tace, ''ku tsaya, baku da tabbas shine ya dauka kawai kuna zargin sa ne tun da kunce shine ya dauka naji Shi dinne nawa ne kudin naku".

"Dubu uku ne ba yawa biya zaki yi ne?"

Bata yi magana ba sai hannun da tasa a jakar ta ta dauko kudin littafin ta ta basu, sai da suka kirga suka gani dubu uku cib.

Wani yace, "Allah ya taimake ka da yau mun ballaka wallahi gayu muje kawai.

Kallan su tayi har suka wuce su biyar reras suna dukan Shi akan wata dubu uku kawai girgiza Kai tayi, ta juya zata tafi taji an rike Mata Hijabi ta baya. Zuciyar ta taji tayi wani irin bugu fiye da na dazu cak ta tsaya bata juyo ba bata tafi ba kamar yarda shima be saki hijabin ta ba Ji tayi a hankali yace, "please help!"

Hijabin ta ta kwace zata tafi da dan sauri ya kuma kama kasancewar beda karfi ko kadan be iya rike hijabin dakyau ba,Yana numfashi sama-sama.

Yace, "please don't go help!"

Juyowa tayi kadan ta kalle Shi taga yarda yake rufe ido Yana nishi sama-sama kamar mai asthma kallan Shi take tana tunanin taimakan Shi ko kuma ta barshi a wurin ga hadari data gani wanda Sam bata San da Shi bane ko bata lura ba sai yanzu, shikuma be fasa fadan Help ba a hankali ta saki wata boyayyiyar ajiyar zuciya kafin ta karasa wuri shi ta tsugunna.

Tace, ''tashi mu tafi".

Dakyar ya uya bude idan sa da suka irine daga Kalar su zuwa Kalar ja, sai da ya gaban ta ya fadi ganin idan sa bata kuma fasa kallan sa yarda shima ita yake kallo Yana lumshe idon sa gaba Daya sai taji jikin ta ya dauki rawa sosai da sauri ta tashi zata tafi ya kuma kama hijabin ta ta tsaya.

Yace, "please!"

Shahada tayi kawai ta juyo ta kuma tsugunna wa tace, "tashi mu tafi".

"I can't". Ya iya fada yana cigaba da nishi.

Kallan bayan ta tayi taga ba kowa ta kuma kallan gaban su namma babu kowa, a hankali kuma taji bugun zuciyar ta na raguwa iska ta fuzzar sannan ta tashi ta kuma rataya jakar ta dakyau ta fara kiciniyar daga shi ta dashi zaune kawai tayi don gaba daya ya sakar mata nauyi gashi babu wani karfi a jikin Shi.

Samun kanta tayi da cewa, ''wai Kai ba zaka kokar ta Ka tashi bane kabarni sai wani fama nake da kai wallahi zan tafi ba barka daman kaga da hadari a garin ruwa ya Zane ka a wurin ba ruwa na Ka tashi taam".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now