*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 24📑*
*__________📖* Be d'auke idan sa ba yana cigaba da kallan ta kamar yarda shima be d'auke hannun sa ba.
Yaya yace, "Yana da taurin kai ko?"
Mizi yace, "Ya jiyo yaga abinda zan masa".
Yaya yace, "kunne ne yake ji".
"Ka rabu da ita ka kyale ta ka dena bin ta haka bata ka bace ba kuma zata taba zama taka ba har abadan abadina".
Kulle idan sa yayi yana tuna kalaman Mahaifiyar sa, babu abinda yake hangowa sai ita dashi lokacin yana yaro tana fad'a masa.
"If some one is strong enough to bring you down, showthem you are strong enough to get back"
Yace, "what if am i detained?"
Murmushi tayi masa Mai kyau.
Tace, "know that the pain will pass and when it does you will be stronger".
Be karasa tunanin sa ba yaji.
Mizi yace, "juyo mana?"
Kansa a kasa ya juyo a hankali ya juyo yana juyowa yaga zai saura kiris ya luma masa wuka a hannun sa yayi saurin rike hannun Yana kallan Mizi.
Yaya yace, "cika masa kawai normal ne".
Tana Jin haka taje wurin su zata taba shi Yaya ya rike ta ganin sai kokaran kwace wukar yake shikuma kokari yake ya luma masa a cikin sa, ganin haka yasa ta gantsarawa Yaya cizo a hannu ba shiri ya sake ta yana rike da ita dan ba laifi yaji cizo, kafin ya farga ta cire takalmin ta mai d'an tudu ta kwad'awa Mizi a kai.
Shima sosai yaji zafin duk da be wani mai tudu bane can amma de da zafi tun da iya karfin ta zage ta kwad'a masa, bashiri ya saki wukar, Yaya yaga zai karaso da sauri ya rike hannun ta sukayi wani layi suna shiga ya shigar dasu wani lungu a tsakanin gidan kamar gidan mutum daya ake yi amma ba'a hade ba, numfashi suke saukewa tare tare da jiyar zuciya ita de jikin ta b'ari yake sosai dan tayi mugun tsora ta da wannan lamari.
Sai da ta dai-dai ta nutsuwar ta ta kalle shi.
Tace, "Kai wai sai yaushe zaka fara fad'a ne? wai ace sam mutum beda k'arfi ko kad'an? har ma na fika k'arfi".
Kallan ta kawai yake shi ba abin yayi magana ba yanzu tayi masa masifa yafi ma kawai ya kyale ta tunda yaga samun bakin magana tayi d'azu ai bega tayi wannan d'in ba.
"Meye kake wani kallo na? nida kake gani na fad'a gare ni tamkar Aruna Irani haka nake yiwa maza duka ba ruwa na".
Kallan ta kawai yake yana jinjinawa alamar naji.
Ladern da ta bashi ya d'auko ya bud'a yaga dambun nama ne ya d'ibi dak'an a hannun sa yasa a baki ya d'aure ya mayar da sauran.
Tace, "ba wanke hannu kawai daga d'auka sai sawa a baki ba bismillah bakomai".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...