12

83 14 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023





*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*

*1441H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

*SHAFI NA 12📑*

*__________📖* Kimamin sati daya Kenan Siyama na zuwa makaranta tun ranar da suka zauna wuri daya dashi Basu sake Zama ba sabida da wuri take zuwa shikuma late, yayin da take Zama a farko shikuma karshe yanzu ta samu kawa sai dai bawai irin saban nan ba suke basa wata maganar arziki Daga sannu sai sannu shikenan abin da yake hadu sai kuma abinda Basu gane ba ita Fatima a hostel take ita kuma day.

A bangaren Sameer kuwa kullum Yana neman hanyar da zasu hadu amma basa haduwa sai dai yake ganin ta koda yazo zaiyi mata wata hanyar take canza wa gaba daya abin na damun sa ya rasa yarda zaiyi har ta littafin ta dayake so ya bata taki bashi wannan daman, be taba damuwa Akan komai ba sai Akan ta rashin maganar da take masa Yana mugun damun sa gashi ko Zama yanzu tade nayi ya Rasa yarda zaiyi.

Yau takama Thursday guda daya suke da ita ya kuma kudura a niyyar sai ya mata da wannan niyyar yau ya tashi.

Yana nan zaune Yana duba handout din sa da ya siya da'ace yana da data da yayi googling wani abu, Amma babu shima yaga yarda zaiyi karatu da naira dari, handout din ma tarawa yayi ya siya.

Tashi yayi yaje yayi wanka ya fito wardrobe ya Bude yaga tsirarun kayan sa Basu fi kala biyar ba sunyi squeezing ba kadan ba, kallan kayan sa yayi dake zube a dakin gashi babu klin bare ya wanke, waist din sa ya rike Yana Yasa hannun sa a cikin sumar kan sa wacce ko tajewa bata samu ballan tana aje ga su Mai gyaran gashi, iska ya furzar Yana girgiza kan sa kafin ya ciro wata t shirt fara yasa ka ya yasa blue din wando abin sa ya fice tare da daukan handout din sauran tarkace ya rike a hannu ya fita Yana fita
Yaga Hajjaty zaune ta kame tana kallo yasan da cewa ta ganshi yau kawai 'yan Kasaitar ne a kusa shiyasa bata masa magana ba, kamar kullum shima ba maganar ya mata yaje ya zauna kusa da ita.

Yace, "Kudin makaranta".

Ko gado Kai batayi ta kalle Shi bare yasa ran amsa yasan kuma taji sai ta gama ja masa rai, shikuma baya so yau ya yayi sallah a gida ma so yake ya tafi da wuri, sai da suka share Sama da minti goma.

Tace, "je Ka dauka".

Shima shiru yayi beyi magana ba irin beji din nan ba.

Yace, "ina?"

Wani banzan kallo ta wurga masa, cike da masifa.

Tace, "Ai ba kallo na kake ba shiyasa Baka San ina nuna maka wurin tv ba zaka sa Kaina yayi ciwo".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now