*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 28📑*
*__________📖* Yau ta tashi da zazzafan zazzab'i sakamon kwana da tayi da tunanin abinda Mujahid yace, wai wanda suka sace ta aka zo nemawa aure tunanin ta d'aya shine yanzu idan Daddy ya duba nagarta Mahaifin su aka bada ita fa? ya zatayi da son wanda bata san tanayi ba sai da aka an karar da ita? da wannan tunanin da damuwa ta kwana gashi ta wuni bataci abinci ba ita da bata da iya wa koda aka sace ta batayi wannan zazzabin ba haka.
Ganin shiru shiru bata sauko ba yasa Baffa shiga d'akin a kwance kuwa ya gan ta cikin blanket tana rawar sanyi k'arasawa wurin ta yayi ya zauna bayan fuskar ta.
Yace, "Meyasa sameki?"
Bakin na rawa.
Tace, "ciwon kai".
"Kinsha magani?"
Ya fad'a cike da kulawa, girgiza masa kai tayi wayar sa ya d'auko ya kira Muhajid yaji ko ya gama ya fito daga exams yace ma gashi nan zuwa ya kusa Mama ya kira yace mata gasu nan zuwa Siyama ba lafiya.
Mujahid na zuwa kuwa yasa ta a mota suka nufi asibiti sai da aka bata abinci taci ta k'oshi sannan sannan aka sa mata drip tare da allurai a cikin sa dan danan bacci ya d'auke ta.
Muhajid yace, "Yanzu meye abin yi?"
Baffa yace, "Inaga Daddy zamu tara da maganar".
"Daddy ko Abba?"
"Daddy de, Abba ba lalle yana gida ba".
"Muje de mugani kasan ai ba kullum ne suke fita ba".
"Muje tou".
Gidan Abba suka nufa sunyi kuwa sa'a yana nan dan mai gadin suka tambaya yace musu yana nan, kamar gidan su duk ranar aiki ba'a samun kowa sai dai idan sa'a akaci Anty ce kullum take gida.
Tana zaune a parlour suka shigo da sallama.
Tace, "A'a wannan zuwan de na Siyama ne itace take saku zuwa".
Murmushi sukayi kansu a k'asa suna gaida ita.
Tace, "Kuma tana ina?"
"Tana asibiti".
"Subhanallah meya same ta?"
"Zazzab'i".
"Ayyyaahhhh gashi bata iya zazzab'i ba, Allah ya sauwake".
"Amin".
"Abba fa?"
Suka fad'a a tare.
"Yana d'akin bak'i, bak'i ne suka zo d'azu ma Daddyn ku yazo shima".
"Bari mu jira shi".
"To shikenan ku tashi kuje ku d'auki abin sha mana ko dan kunga ba kowa?"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...