29

65 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 29📑*



*__________📖* A dai-dai gidan aka sauke shi ya biya mai napep kud'in sa ya bashi canjin sa yasa a aljihu, a hankali ya tura k'ofar gidan ya shiga d'akin mai gadi ya kalla yaga baya nan alamar ya tashi tun da lokacin an kira la'asar maybe ya tafi ya alwala ko kuma ya ma tafi masallaci ta inda ya fito ranar da ya kawo ta tanan ya nufa ta, cike da sand'a yasa kai zai shiga ya hango Mujahid shikuma hannun sa rike da key komawa yayi dasauri sai kuma yayi sauri ya dawo ta k'ofar gaba gaban na fad'uwa amma idan ya tuna zai ganta sai yaji wani irin dad'i na ratsa shi da farin ciki duk da be tabbatar da lafiyar ta k'alau ba.

Yana tsaye a balconyn shi be shiga ba shi kuma beyi knocking ba, Mujahid ya fito shida Baffa kallo d'aya Mujahid ya masa ya gane shi yana rufe gida.

Baffa yace, "Lafiya?"

Sunkuyar da kan sa k'asa yayi.

Yace, "Sannun ku".

Baffa yace, "yawwa".

Mujahid yace, "wa kake nema?"

A hankali cikin sanyin muryan.

Yace, "Maryam".

Baffa yace, "Maryam wa?"

"Hussain".

Muhajid yace, "Ayyyaahh kaga kuwa bata nan amma lafiya?"

Murmushin da yasa ba yi kullum yayi ya d'ago da kan sa yana kallan su.

Yace, "daman na zo ganin tane naji kamar ba..."

Sai kuma yayi shiru jin yana neman wuce gona da iri zai yi sub'utar baki, sai kawai yayi murmushi suma murmushi sukayi.

Mujahid yace, "Aikuwa kaga bata nan".

Baffa yace, "wa za'a ce?"

Shiru yayi ya kauda kan sa alamar de beji dad'i ba sai kuma ya juyo da murmushi sosai a fuskar sa.

Yace, "Sameer".

Ko kuma kawai kuce.

"Cowardiiiice".

Yarda ya fad'a zaka san lalle beso rashin ganin ta ba dan har wani k'yalli idan sa ya fara.

"Shikenan Insha Allah za'a fad'a mata, bari muje zamuyi sallah".

Murmushi yayi musu yana ganin su suka wuce shi zasu tafi.

Yace, "ga wannan".

Juyowa sukayi suka tsaya ya mik'a musu Mujahid ya ansa.

Yace, "a bata".

Baffa da ya karb'a ya bud'e ya ga abinda ke ciki yana kallan shi kuma yana murmushi.

"Har kun saba da ita haka? kasan me take so?"

Mujahid yace, "Kana san ta ne?"

'Dauke kan sa yayi daga gare su ya mai da k'wallar sa sannan ya juyo da murmushi fal fuskar sa, ya d'an girgiza kai tare da kad'awa.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now