25

76 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 25📑*

*__________📖* Washegari   tare da Sultan suka tafi makaranta tasan kuma baza su dawo ba tunda jiya an fad'a musu da bata nan ita de badan ta so ba wannan tsarin ba da aka canza ganin ta da Sultan yasa Malam Iliya bai tsaida ta ba sai kallo da ya bita dashi ko kallan sa batayi ba bare yasa ran su had'a ya sakar mata murmushin dake kara mata jin haushin sa,
a d'ayan b'angaren kuma tana san ran yau ma zai zo su had'u da wannan tunanin yau take karatu.

Sha biyu  na rana Abba da Daddy na zaune a wurin hutar dake bayana gidan sosai suke hira dan Abba ya jima bezo ba saboda tafiye tafiye da ga masa yawa Baba mai gadi yazo.

Yace, "Alhaji kayi bak'i".

Daddy yace, "Nikuma?"

Abba yace, "kace kawai su shigo kasan wasu bak'in surprise suke yi amma mata ne ko maza?"

"Maza ne".

Daddy yace, "kawo su nan".

Yace, "Sam bansan da zuwan su ba".

"To so kasan wasu haka ne ni inaga ma tunda kayi bak'i tafiya zanyi".

"Ka tsaya de ku gaisa dasu".

Beje gayin magana ba suka karaso tare da Baba yana musu jagora su uku, tashi sukayi cike da girmamawa suka k'arasa wurin su tare da mik'a musu hannu ganin su manya dasu sai da suka zauna sannan Daddy ya tashi ya shiga ciki.

Mama na zaune a parlour.

Yace, "Nayi bak'i a d'an had'o musu abin motsa baki".

"Kaga kuwa na gama abinci ko zuba musu ma za'ayi?"

"Ehh amma a fara kawo ruwan de tukunna".

"To bari na bawa Baffa da Mujahid su kawo".

"Yawwa sannu da kokari".

Murmushi kawai tayi ta nufi kitchen shikuma ya koma ta kofar daya fito ta baya, sosai Abba ke jansu da hira shida yace zai tafi sai da ya zauna sannan suka Kara gaisuwa.

Daddy yace, "Sai dai shaida ku ba".

'Daya daga cikin su.

Yace, "Da farko de ni sunana Shehu wannan kuma sunan sa Hassan da Adam k'annain suke a wuri na kuma bakomai ya kawu mu nan ba sai neman aure".

"Aure kuma?"

Daddy da Abba suka mai-maita.

"Ehh muna nemawa d'an mu Muzzafar auren 'yar ku Maryam".

Dai-dai nan Baffa da Mujahid suka karaso gaba d'ayan su sai da k'irjin su ya buga jin wannan al'amari shi kan sa Daddy sai da k'irjin nasa ya buga Abba kuwa dariya yayi yana kallan su.

Yace da su Baffa.

"Yawwa ku karaso ku ajje musu yanzu ma zasu shigo su abinci ai ku kawo maza maza ku zuba musu".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now