35

77 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 35📑*

*__________📖* Bashi ya dawo ba sai wurin shabiyu na dare shima yana tafiya yana tangad'i kana gani zaka san ya bugu a haka ya shigo gidan har sannan Hajjaty na jiran dawowar sa ganin sa a haka ba k'aramin haushi taji batare da tayi tunanin komai ba ta tareshi ta wanke da wasu lafiyayyan maru, marin da yasa shi ya fad'i daman ba k'wari ba.

Tace, "Dan uwar ka harni zaka karyawa doka a cikin gidan nan waye kai? kana so naji kunya ne? kana so ka tozarta mu ko?"

'Dago idan sa yayi yana kallan ta tuni yaga ta koma masa Garrulous ranar da ya fara ganin ta ranar da ta fara masa fad'a ranar da be manta taba a tarihin rayuwar sa, yana kallan ta kawai ya fara murmushin tare da dariya ita kuma sai fad'a take ganin yana dariya.

Tace, "wato banza ka maidani ko?"

Tashi yayi yana shan giyar sa yayi gaba yana cigaba da dariya har yaje dakin sa yana zuwa ya kwanta a k'asa tare da kallan d'ankwali dake yashe wanda yasan shine ya jefar ya d'auka sai kuma k'walla ta cika idan sa lokaci guda kuma  ya dawo hayyacin sa.

"Garrulous, kin tafi barni bazan sake ganin ki ba?"

Tashi zaune yayi tare da d'auko hotan Maman sa yana gani, ya goge hawayen sa wani na zubo daga idan sa yana kuma shafa hotan da hannu d'aya.

Yace, "Ammaahh...

Sai kuka, ya kasa furta abinda zai fad'a, k'ara goge hawayen sa yayi da bayan hannun sa ya kuma shafa hotan yana hawaye bakin sa har rawa yake kamar wanda aka masa dole sai fad'a.

"Kin..ta..fi..kin..bar..ni..."

Sai yayi shiru yana cigaba da kallanta tare da kuma goge hawayen.

Yace, "gashi yanzu itama ta tafi ta barni i taught  she is my happiness but she's no longer, she's not the one, you was always telling me wata rana sai labari, I still don't understand what you mean".

Shiru ya kuma yi sakamon hawayen da yaci k'arfin sa.

"Kinsan me Ammaahh?. Do you know what the worst part of me?"

Goge hawayen sa yayi yana jan majina.

"Is missing her, every time i try to tell myself to stop missing her or think about her i couldn't, and you  too Ammaahh".

K'ara kwanciya yayi ya rungume hotan a kirjin sa yana kuka cike da k'uncin da yasan bazai tab'a barin saba ba a hankali wani tunani ya fara zuwar masa to meye ma amfanin rayuwar sa, me yasa yake rayuwar? abinda ya tambayar zuciyar sa kenan.







☘️







"Mom yaune fa aka d'aura wa yarinyar nan aure imagine".

"Yaya kasan nifa damuwa ta yanzu shine kawai mu same ta, idan muka same ta komai yazo mana da sauk'i wannan karan bazamu tab'a yarda ta kub'uce mana ba".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now