🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•**SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''
*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SHAFI NA 57📑*
*__________📖* Rufaida ta girgiza kai cike da tausayawa sam ta kasa gane menene inda matsalar ta dosa ajiya tazo gidan amma daga jiya zuwa yau taga abubuwa da dama bata ga wani sight effect ba na Mom koma tace bata san shi ba amma gashi Hainasu na fad'ar wata magana haka ma Ummi wannan wacce irin rayuwar ce sukeyi haka a cikin gidan nan?
Mom kuwa wani irin tarin bak'in ciki ne ya turnik'e ta maganar yarinyar ta yau yafi komai d'aga mata hankali, babban bak'in cikin ta shine a haka zasu ci gaba da zama da ita? Shiga d'aya fita d'aya sai tayi magana? gashi yau ta kasa tanka mata, ta kasa tsawatar mata a hankali ta d'aga k'afa ta fara tafiya batare da ita abinda takeyi ba.
Rufaida ganin Mom ta tafi ta kalli Hainasu.
Tace, "Idan har Mizi yasan abinda kika yiwa Mahaifiyar sa bazai tab'a jin dad'i ba, Hainasu Mijin ki ya canza ya kamata ace kin san da wannan Haina, ki canza kiyi zaman lafiya da ita..."
"Kinga tsaya bawai wa'azi nace kimin ba, ko nasiha naji zan gyara idan ita ma ta gyara nasan abinda ya kamata da wanda be kamata ba".
Daga haka ta tashi ta bar wurin girgiza kan ta Rufaida tayi ta tashi ta shiga d'akin Mom a zaune ta ganta tana danna waya sallama tayi ta k'araso a gefen gadan ta zauna tayi shiru.
Mom tace, "Rufaida lafiya?"
"Mom daman abinda ya faru ne tsakanin ki da Hainasu".
"Inaji".
"Mom me zai hana ku dawo tamkar 'ya da uwa keda ita..."
"Tashi ki fita".
"Mom..."
Cike da tsawa ta maimaita ta dorawa da cewa.
"Gulma ya kawo ki gida na ko? idan ba gulma ba uban me ya kawo ki ina ruwan ki da yarda muke zama a gidan nan".
"Mom..."
"Ke! wato uwar kice tace ki zo ko? ki gyara gidan, ki fara gyara naku gidan kafin kizo ki gyara kuma ki tattara yanaki yanaki ki fice min daga gida kafin mijina ya dawo".
"Fita".
Wani iri sororo Rufaida tayi tana kallan ta wato bata san halin ta ba har take ambato uwar ta a zancen lalle idan bata taka mata burki ba juyawa ta zatayi kafin gobe tayi ta bar gidan.
"Dan uwar ki ina maki kina jina..."
"Mom ya isheki haka nan, uwa fa bata fi uwa ba da zaki sani a gaba dan maki zancen gaskiya, ato babu yarda za'ayi ace daga zuwa zan maki magana kisa uwata a zancen ki ato ni da kike gani nafi Hainasu rashin kunya da rashin ta ido, kuma gida bazan tafi ba tunda gidan Ubana ne ehe".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...