🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•**SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''
*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*Last page
*SHAFI NA 62📑*
*__________📖* Sai da suka tsaya a Arewa Dandi sukayi sallah tare da bankwana da mutanen gidan Shuguba bayan Shugaba ya musu nasiha sosai a kan zumunci rashin zamunci ne yasa aka manta da Hajjaty haka rashin zumunci ne yasa duk abinda ya faru da Maryam ya faru da'ace ana zuwa da ansa halin da take ciki da kuma tuni an magance ta, haka ma da zurfin ciki da rashin fad'ar matsalar dake damun ta da duk abinda ya faru be faru ba duk da Allah yasa hakan zata faru a rubuce yake.
Duk wannan bidirin Hajjaty bata san anayi ba dan a bayan mota aka barta tana bacci gashi taji ac ta kuma cika cikin ta tuni baccin ta ke mata dad'i bata san ma inda take ba.
Siyama kuwa bata san tana ciki ba sai da suka zo tafiya ta juyo da kanta ta ganta, sun fara tafiya lokaci.
Tace, "Cowardice mun shiga Uku, ka tsaya wallahi Mahaukaciya ce ta shigo mana mota, wai ina maka Dan Allah ka tsaya mahauciya ce fa kalla kaga bayan motar mu".
Juyowa yayi ya kalle ta aikuwa bata da maraba da Mahaukaciyar sai da yayi murmushi.
Yace, "Hajjaty ce fa".
"Hajjaty?"
Sai kuma ta juyo tana kallanta ita de bata ga kallar Hajjaty anan ba.
Tace, "Gaskiya Cowardice ba Hajjaty bace, kalle ta fa ka gani nide gaskiya bazan zauna a motar nan ba da Mahaukaciya taab to kezai kawo Hajjaty nan?"
"Daman ba Daada yace tana k'auye ba? Shugaba ya kawo ta taga 'yan uwa? to maybe shine ya zama haka".
"Cowardice nikam tsoro nake ji gaskiya ka tab'a ganin Mahaukaciya kuwa?"
Dariya yayi sosai, ya kalle ta yarda ta tsure gaba d'ayan ta ta kalli baya ta kallo titi tana magana jikin ta kawai karkarwa yake ga idan ya fito yayi k'wal k'wal dashi me kuwa zaiyi ba dariya ba.
Tace, "Wallahi ba zancen wasa ba, yanzun idan ta maka wani damk'a babu Wanda zai k'wace ka sai Allah".
"A'a ta maki de, ni ina ruwa na da ita kece kika ce mata Mahaukaciya kinga tana tashi zata ji Fadi dank'ar wuyan ki".
"Haba Cowardice meye haka?"
"Menayi fa?"
K'ara Hajjaty tayi da sauri ta d'auke Kai ganin tana kifkifi da ido.
Yace, "kuma idan kika k'ara magana shikenan mu duka mu zata had'a ta shak'e".
"Na dena Allah kuwa na dena".
"Yaww gwarade My Cowardice".
Cubo baki tayi gaba ta fara gunguni.
"Ko bake bace?"
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...