30

87 8 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 30📑*



*__________📖* Mujahid yace, "Daddy mene had'in Hajjo da zazzab'in Siyama?"

Siyama tace, "Idan zata zo Yaya kace ta taho min da kajin kiwo..."

"Bazaki mayar ma da gida gidan kiwo ba nan gaba kuma tinkiya zaki ce gaba gaba gaba kuma shanu da talatalo".

"Kasa Daddy ta kawo min talatalon ina so na fasa kajin".

Ta fad'a tana washe baki irin ka tuna min d'in nan.

Daddy yace, "shikenan to zan fad'a yanzu bari naje wurin Doctor d'in".

Yana fita suka bita da harara, ta cigaba da cin cocos d'in ta.

Tace, "oho de d'an bak'in ciki sai dai ya mutu".

"Dawa kike?"

Mujahid ya fad'a yana b'allo mata harara.

"Allah sarki ni da wancan mai k'atan kan nake".

Sultan yace, "Dan kin renani ko?"

"Ya Mujahid kaji shi ko? yaran nan ya rena ni, sai da fa na bushe a gidan duniya sannan kazo da wayo na aka haifeka zaka ke rena min hankali dan kaga bana san Anty ko Yaaya shine kake wani cika baki ka cigaba indai nice hmmm".

Mujahid yace, "ke wai idan kinga baki da lafiya kinfi kaud'i da fitsara ko?"

Turo baki tayi gaba ta ajje cocos ta d'auki sweet tana sha tak'i yarda ta kalle shi tasan mugun kallo yake mata daga k'arshe ma gunguni ta fara yi ita d'aya sai kuma ta kalle shi.

Tace, "Ya Mujahid wai ina Anty Zainab ne?"

Hararan da ya zuba mata ne yasa ta sunji da kan ta tana tsotsar sweet.

Daddy yace, "Mujahid bana san zaman ka anan saboda cin zalin ta kawai zakayi yanzu nasan kayi mata wani abu".

"Daddy ba abinda na mata".

"Ku tashi mu tafi".

"Daddy har yanzu fa jikin ta da zafi sosai".

"Doctor ai ya bamu magani da allurai ko? Babana?"

Shiru yayi yana sunkuyar da kan sa k'asa, kafin ya taimaka mata ya sauko da ita yasa mata hijibi bata da takalmi dole sai dai ya d'auke ta.

"Na goya ki?"

Tsayuwar da sukayi wanj irin jiri take ji, cike da washe baki.

Tace, "Ehh daman koda ina yarinya Hajjo tace ko d'auka na baka yi".

Ganin Daddy na kallan su yasa shi yin k'aramar k'wafa ya sunkuya ta hau bayan sa ya goya jikin ta zafi gau dan jikin sa sai da ya d'auki d'umi ita kad'ai tasan me take ji a jikin ta amma take musu abinda taga dama, a baya yasa ta bayan sunje wurin motar Daddy shikuma ya tafi siyo magani hakan yasa ya bawa Sultan key d'in.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now