7

117 15 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023











*°🔘° A RAYUWA MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰

*TUKUICI GA:* sweetheart😘

*Zulfa'u Kabir this page is for you* 🥰

*SHAFI NA 7📑*

*__________📖* Washegari da safe bayan sunyi sallah suka koma bacci har Anty ta tashi ta shirya tana bacci sabida tunani da tayi jiya da daddare hakan yasa take ta bacci abinta tana cikin bacci taji Mama na tashin ta.

"Siyama ki tashi fa kina da zuwa islamiyya, tashi Maza da sauri".

Tashi tayi tana cuno Baki.

"Mama fa naga yau Monday".

"Kin tashi ko sai zabga maki tafi".

Saukowa tayi tana Zumbura baki gaba ta Shiga toilet Zama mama tayi a bakin gadan.

"Ki fito ki same ni anan ina jiran ki".

Bata wani jima ba ta fito ganin mama zaune yasa ta yi gaban mirror ta  sai da ta goge jikin ta shafa Mai kadan taje tasa kayan ta.

"Dauko tsintsiya da mopper".

"Mama yunwa nake ji".

Ta fada tare da ya mutse fuska, kallan da Mama ta wurga mata yasa ta yin saurin nufar kofa taje ta dauko a gaba mama tasa ta sai da ta gyara dakin tsab haka ma toilet ta fito da kayan su ta hada na wanki sleeping dresse da inner wears ma ta hada ta wanke toilet din sai da ta wanke Shi sau uku tana yi Mama na cewa ta sake.

"Wayyooo Mama baya na Kinji ciwo? Amma de bazani makaranta ba ko?"

Harara mama ta balla mata tayi hanyar fita, itama biyo ta tayi tana cewa.

"Allah Mama baya na ciwo yake min ga Shi naje Nayi ta Zama ga yunwa ma nake ji".

"8 zaki kike tafi ranar Monday to wednesday ki dawo 12".

"Amma Mama..."

"Nafa nasan shirme".

"Laa Mama nifa haka zance Ina yaya na Mai Sona?"

"Zan ranki yake ki tashi daga bacci ya tafi aiki".

Turo baki tayi gaba lokacin sun kawo kitchen ganin Mai aikin su tana ta aikin ta yasa suka gaisa Sama Sama da ita tabi bayan Mama da ta fito da flask sukayi dining tare suka ci abinci tana Mata zuba suka Gama ta kwashe kayan ta Kai kitchen.

"Mama yau Baki da aiki ne?"

"Sai 2".

"Aww nace to ko zaki kaini ne sai ki musu bayani".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now