55

100 11 0
                                    

🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍

*1442AH/2020M•*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•*

*SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''

*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 55📑*

*__________📖* Shiru ba'a d'aga ba, ya kuma kira nan ma ba'a d'aga ba cigaba da kira yayin da suka samu wuri suka zauna kowa a k'asa yana ta cigaba da kira ba'a d'agawa wayar ya sauk'e yana kallan su cike da tausayawa suma shi suke kallo, kafin Daddy ya ansa wayar yayi dialing sai dai shi ko shiga ma batayi ba wai a kashe aka ce masa jikin sa matuk'ar sanyaye ya ajje wayar yana tunanin ina suka shiga haka ne?

Abba ne ya shigo shima kana ganin sa zaka ga damuwa a tare shi kallan su yayi kawai yarda suka wani cunkushe a wurin d'aya kamar masu jiran wani abu, babu wanda ya iya cemasa komai, ganin haka yasa cewa.

"Hussain".

Jin haka yasa Daddy tashi ya zauna a kusa da shi yayin da su kuma suka nemi tafiya ya tsayar su.

Yace, "Nasan kana rik'e dani a zuciyar ka har yau idan ka tuna nine silar faruwar komai ko?"

Daddy be d'ago ya kalle shi ba bare ya tanka masa tsoron abu biyu yake ya rasa Maryam k'auwar sa yanzu kuma beso ya rasa Siyama 'yar sa a karo na biyu akan wani zancen da bekai ya kawo ba sun bar gida.

"Yau ina fatan zaka wanke wannan abin da yake zuciyar ka naso ace ba yanzu zan fad'a ba sai dai yarda Hajjo ta damu da Siyama bata damuwa da mijin ta yasa zan fad'a maka ko zaku damu dashi shima".

"Kasan Mijin Siyama waye a wurin ka?"

Girgiza kai Daddy yayi yana me kallan Abba, murmushi yayi ya girgiza kansa.

" 'Dan k'auwar ka ne, MARYAM".

Ba Daddy har Sultan sai da suka ji maganar kamar al'amara taya hakan ya faru? kowa abinda ke cikin zuciyar shi kenan, Daddy kuwa kallan sa kawai yake yana tunanin anya kuwa gaskiya ne zancen nan? to amma abin tambayar anan taya akayi haka? taya yasan shine?.

"Abba yace dogon labari".

"Tak'aita shi".

Daddy ya samu kan sa da fad'ar hakan batare da yasan yayi ba kawai shidai yasan a wannan lokacin idan har ba'a fad'a masa ba to yasan komai zai iya furawa wanda shima besan ko menene ba.

"A wata tafiya danayi zuwa Dubai jirgin mu zai fara Abuja daga nan mu tafi,munje Abuja sai muka fito kafin jirgin mu ya tashi".

"Ina zaune Abubakar yazo ya wuce sai dai ya yardar da wallet d'in sa, na tashi zan kaima kafin na d'auka na neme shi narasa sai na bud'e wallet d'in, hotan shi nagani shida Maryam da jariri a hannun su nagani sosai abin ya bani mamaki ina tsaye a wurin ya dawo da'alama neman ta yayi be ganta ba".

Yace, "Bawan Allah nawa ne, nagode anan nayar ko?"

Murmushi kawai nayi masa na bashi, ya manta ni kamar yarda nima na manta shi, ya tafi abinsa koda muka shiga jirgi sai naga ya zauna a kusa dani hakan ya min dad'i, shine ya fara min magana sannan nima na masa beda wahalar sabo kamar mace haka yake tuni muka saba dashi.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now