37

88 15 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 37📑*

*__________📖*  Tashi yayi a hankali ya sauka daga gadan zuciyar sa na wani irin bugu ya k'arasa kusa da kan ta ya zauna yana kallan fuskar ta ta da take a rufe hannun su batare da wata fargaba ba ya cire mata hijabin dakyar dan ta nannad'e hular dake kan ta ma ta cire, ya k'urawa gashin kan ta kan ta ya kasa lek'a fuskar yagani ita ce ko ba ita bace? kamar ance ta juyo ta juyowa da fuskar ta tana yatsine fuska wani irin zabura yayi yana k'ara hawa gadan kawai fuskar yake kallo yana dariya dariya murmushi murmushi ya kasa tantance wanne zai yi daga ciki sai kuma wani siririn hawaye ya zubo a fuskar sa yasa hannu ya share yana cigaba da kallan fuskar ta.

Gani yayi tana juyi da k'afar ta bashiri ya koma wurin k'afar ta ya cigaba da danna mata cike da wani irin farin cikin da ya kasa b'oyewa a fuskar sa daman gashi fuskar sa abokiyar murmushi ce tsayawa yayi da danna mata k'afar sakamon wani tunani da yazo zuciyar shi.

"Idan kuma bak'uwar Mommy  ce fa? yasan basa nan k'ila shiyasa Hajjaty ta turo ta nan".

A hankali duk wani nishad'in dake cikin zuciyar sa wanda ya wanke duk wani k'unci da kad'ai ci da yake ciki ya fara dawowa yana baibaye wannan farin ciki da kuma nishad'in dake cikin ta lokaci guda idan sa ya kawo k'walla ya sauka a gadan ya nufi hanyar fita, a parlour ya kwanta yana cigaba da tunani a haka bacci ya d'auke shi.

Washegari da safe ba ita ta tashi ba sai goma da mintuna tana tashi ta shiga toilet sam bata lura da kayan dake yashe a cikin toilet d'in ba da tayi sallahn asuba sai yanzu ta kan su, girgiza kai tayi tare da kwashe su ta zuba a laundry sannan ta wanke toilet d'in tas tayi wanka ta fito ta gama shiryawa tsab tana k'ara shafa turare ya shigo jin an bud'e k'ofar yasa ta juyowa shima hannun sa rik'e da d'ankwalin ta ita bata tashi ba ita bata dena kallan sa ba, zuciyar ta kawai taji tana bugawa me cowardice yake anan sai kuma tabi hannun sa da kallo.

Murmushin k'arfin hali ya sakar mata yana k'arasowa.

"Har kin tashi? tun d'azu nake so ki tashi ki fad'a min inda kika sa akwatin nan ta kan gado sai kuma nagani ma, sannu da k'ok'ari".

A hankali ta tashi tsaye tana cigaba da kallan sa.

Tace, "Co..war.. di..ce? me kake anan?"

Wani murmushin ya kuma ya ya fara takowa wurin ta.

Yace, "nida d'aki na? ke zancewa me ya kawo ki nan?"

"Kamar ya?"

"To ke me kike anan? ina de Mommy idan zatayi tafiya bata kulle part d'in ta, d'akin Rufaida a bud'e to me kike anan?"

Shiru tayi tana wani tunanin.

Tace, "kenan kaine miji na?"

Dum k'irjin sa ya buga tare da waro ido yana cigaba da kallan ta.

Yace, "ah haba de wasa kike ni da ko fad'a min ba'ayi ba? za'amin aure gaskiya bani ba maybe ba Haidar ne".

Wani irin tukaici ne taji ya kamata kenan baya san ta a matsayin mata amma ya iya kukan rabuwa da ita bata san da ta wani wurga masa harara ba.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now