13

82 13 0
                                    


💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023








*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

*SHAFI NA 13📑*

*__________📖* Karfe shida nayi Mujahid yaje zai dauko ta dayake be koma gida ba Yana cikin school din, Yana zuwa yaga ba kowa a wurin ko irin alamar mutane anyi lectures ana watsewa babu kowa a wurin, fitowa yayi Yana duba wa bega kowa ba.

Yace, "to ko tana hostel? Bari na tambayi kawarta".

Shiga motar yayi yaje har bakin hostel din su ko Allah zai sa ya ganta, fitowa yayi Yana dubawa ya ganta kuwa tana tahowa zata je hostel din, Dan sauri yayi yaje ya tare ta.

Yace, "Fatima Ina Maryam?"

"Ya Mujahid ina wuni".

"Lafiya qalau, Ina Maryam naje theatre bangan ta ba".

"Yau fa lecturer yace bazai zo ba, waya na ya samu matsala ban Kira ta na fada mata ba, muma dazun nan aka sanar damu".

Ta karashe da murmushi a fuskar ta.

Yace, "ohhk nagode maybe ta koma gida bari naje".

"To shikenan Ka gaida ta".

"Zata ji".

Ya fada kamar dagaske zai fada din.

Mota ya Shiga ya tafi ita kuma ta wuce, Yana zuwa gida bene meta ba sultan yagani a parlour Yana kallo da uniform na islamiyya a jikin shi.

Yace, "hala Mama ta fita ko?"

"Ehh fita barka gidan Abba, Anty Sadiya ce ta haihu".

"Okay Allah ya raya".

Har ya wuce yaji Sultan.

Yace, "Ya Mujahid ina Siyama nadawo bangan ta ba, Ya Baffa yace bata dawo ba".

Cak ya tsaya be juyo ba sai ji yayi kirgin sa ya bada wani irin saurin bugun da be taba yi ba a hankali ya juyo yana kallan sultan da ko kallan sa baya yi sabida Kujeran da ta kare, Jin shiru yasa sultan Dan tasowa ya dago da kansa.

Yace, "Ya Mujahid nazaci har Ka Shiga daki".

Ta kowa yayi a hankali har yanzu kusa dashi.

Yace, "kana nufin bata zoba Kenan?"

"Ehh haka ya Baffalo yace".

"Ko tana tare da Mama?"

Sallamar da Mama tayi ta shigo yasa Shi kallan kofar.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now