34

78 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 34📑*

*__________📖* Ta idar da sallah kenan ta kwan ta ta taji kamar motsi a bayan d'akin ta ana so a bud'e k'ofar amma da yake a rufe take an kasa aka koma ta window gaban ta taji ya fad'i sosai a hankali ta tashi ta lek'a bata ganin kowa kasancewar ta jikin k'ofar ta lek'a a hankali ta bud'e k'ofar gaban ta na fad'uwa sosai ganin mutum na k'ok'arin bud'e window, bayan sa kawai ta kalla ta gane shine tsayawa tayi tana kallan sa batare da tayi motsin da zai gane tana wurin ba, ganin ya kasa bud'e windown da'alama shima a kulle yake juyawa yayi da niyyar komawa ta inda ya fito kawai ya ganta a bayan sa ta jingina tana kallan sa shima kallan ta ya farayi sai da ya juyo taga yayi wani bak'in tashin hankali daman gashi ba fari ba sosai sai ya kuma yin duhu ya rame har ta idan sa yayi ciki.

Sauke idan ta tayi daga gare shi sannan ta maida k'ofar ta rufe  ya jingina a cikin ta a hankali ya k'araso kamar Mai m tsoron tafiya hannun sa rik'e da d'an mininin box kamar na zobe idan sa kuwa k'walla ce ke fita ya kalli abun ya kalle ta ganin itama ta fara kukan hannu yasa ya goge fuskar shi dashi sannan ya mik'a mata.

"Kiyi hakuri banzo ta hanyar data dace ba, gashi".

Ya mik'a mata, bata san ansa amma ganin ya tashi ya kawo mata gashi yana kuka ya karyar mata da zuciya hannun tasa ta ansa batare da ta bud'e ba, juyawa yayi zai sauka ta inda ya fito.

"Kukan fa?"

Taji ta fad'a batare data shirya ba tasan zuciyar ta ta tambaya kukan me yake kawai taji maganar ta fito, juyowa yayi tare da yin murmushin mai ciwo yayi cigaba da kallan ta tare da dawowa ya zauna a k'asa duk da bakomai a wurin a haka ya zauna, itama zamewa tayi ta tsugunna tana kallan shi.

"Bansan wanne irin kuka nake ba, ina jin ciwon auren da zakiyi".

Kallan tayi yayi, yayi murmushi.

"Kiyi hakuri, bawai nace ina bak'in ciki ba, amma bansan naganki kin tafi kin barni".

Tashi yayi ya share sauran hawayen sa tare dayi mata wani irin murmushi mai kyau k'walla na k'ara fitowa daga idan sa ya haura ta balcony d'in Daddy, da sauri ta tashi taje tana lek'ashi tana kallan sa har ya tafi tasan yaji wahala duba ga yanayin sa wahalar hawa da kuma wahalar sauk'a.

A hankali ta koma d'aki ta rufe hawayen ta ta goge ganin haske a d'akin taje ta kwanta batare data tsaya ganin waye ya kunna hasken ba, sai dai ta kasa bacci abinda ya bata ko bud'ewa batayi ba ta rik'e shi gam a hannun ta a haka ta k'arashe kwanan nata batare da ta runtsa ba tana kuka tare da tunani.

Sai da tayi sallahn asuba sannan ta kwanta batayi wani baccin kirki ba aka tashe ta gani tayi har sun shirya hakan yasa itama zuwa tayi wanka aka kawo mata taci abinci kad'an a cikin k'awayen ta daman ake mata k'walliya sosai tayi kyau cikin kayan ta, wurin Mama aka kaita ta gaida ta tare da k'awayen ta kowa sai yaban ta yake sannan tace zata je wurin Daddy.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now