🤍🤍🤍*A RAYUWAR MU*🤍🤍🤍
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad @ *HijjartAbdoul.*
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗
*TUKUICI GA:* sweetheart
*SHAFI NA 49📑*
*__________📖* Suna zuwa aka nemi a raba musu gam ta rik'e haka shima yak'i ya saketa.
Police d'in yace, "kaga kasa su kawai idan d'aya yaga yarda ake jibgar d'aya sai d'aya ya fad'i yaran waye".
Ita de sosai take kuka ta rungume shi, shima side hug ya mata kallo ne kawai nashi a cell aka sasu aka rufe kan bench suka samu suka zauna abin su basu damu da cewa nasu bane wanda suke zama idan zasu jibgi mutum.
Suna zaune ta jingina kanta da kafadar sa shikuma yana rarrashin ta sun kasa furta koda kalma d'aya ce a haka bacci ya d'auke ta ba tare da ya sani ba ga wani uban gumi daya feso mata a goshi ga sauro rasa yarda zaiyi yayi shi ba ta shi ba yake ta ita yake duba ga yasan sabida shi ne wannan abun ya faru ita mene nata a ciki da za'a sako ta acikin zancen su?.
Gyara mata kwanciya yayi ya d'aura kan ta a cinyar sa ya matsa sosai farkon bench d'in ya d'aura k'afar ta akai tare da rufe mata ita da hijabin ta yana kuma goge mata gumin da dake kan goshin ta ji yayi an k'ara hasken wuri yana d'agowa kuwa yaga wannan police d'in sai kuma wani a bayan sa da sanda alamar idan sunyi gardama a bige su zama yayi a kujerar daya shigo da ita.
Yace, "Lalle baka tab'a shigowa ba nan wurin zan ma uzuri ganin matar ka tayi bacci".
Kallan sa kawai yayi ya mayar da kallan sa ga Siyama.
"Amsar tambayar ta kawai nake nema yaron waye ka sata? ko nace kuka sato?"
Shiru ba amsa.
"Dole sai da taimakon ta zaka anso tunda ance a gida ne kukayi satar".
Tana bacci take jin magana sama sama da k'arfi gashi daman zafi ya hanata baccin yayi dad'i bud'e idan ta tayi a hankali ganin wannan police d'in yasa ta mayar wa ya rufe sai dai maganar da ya fad'a kamar tana mafarki haka nan taji ta.
"Tambaya ta k'arshe a'ina kuka sato wannan jaririn?"
Namma shiru babu amsa.
"Ohk, bari na tashi Matar ka ko ita zata fad'a amma kasani wannan shine alfarmar k'arshe dan bani da mutunci".
"Sergeant".
Ya fad'a tare da mik'a hannun sa aka bashi ruwa mai sanyin gaske zuciyar sa d'aya ya zaci sha zaiyi ganin ya b'ula be ankara ba yaji wani irin sanyi a jikin sa yayin da ta zubara ta tashi zaune jin ruwan sanyi sam bata san abinda yake nufi ba kenan da yace sergeant.
Kallan ta yayi yaga yarda take yarde ruwan da aka zuba mata tana sauke ajiyar zuciya sabida sanyin ruwan, sosai ranshi ya b'aci sai dai be nuna ba kallan sa tayi taga ita yake kallo hannu kawai yasa ya jawota tare da kwantar da kanta yana bubbuga bayan ta.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...