*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 17📑*
*__________📖* Da daddare suna parlour su dukan su Siyama na kwance akan katifa yayin da su kuma suke kasa su dukan su suna hira fuskar su cike da annashwa.
Tashi zaune tayi.
Tace, "Ya Mujahid ina ice cream din na".
Sai da ya ga kalli Daddy yaga baya kallan su sannan ya galla Mata harara tare da yin kwafa.
Daddy yace, "tashi kaje Ka dauko mata mana bafa nasan irin haka kana gani de bazata iya taka kafar bako?"
Tashi yayi yaje ya dauko mata ya ajje, ita kuwa dama ta samu daman indai bata da Lafiya to haka ne sune masu yi Mata hidima.
Abba ne ya shigo matar a a bayan sa dan ya sanar da ita batan Siyama bayan sunyi gaishe gaishe matar sa Mai Suna maimuna wacce suke ce mata Anty.
Tace, "akan meye za'a ajje ta anan dan kowa yake ganin ta kome?"
Dan kallan ta Daddy yayi har zaiyi magana sai kuma yayi shiru.
Abba yace, "Kauwa ta dafatan de basu maki komai ba".
Idan tane ya cicciko sakamakon tunawa da tayi da dashi da yanzu tana cikin wahala ko kuma ta karye kanta a kasa ta dauko fuskar mutane salihai ta daurawa mata ta girgiza kai tana taba robar ice cream din take sha.
Abba yace, "Zaki iya tuna Wanda suka saceki?"
Shiru tayi tana nazari ita kadai a zuciyar ta yayin da Abba yake kallan ta cike da tausayawa can ta dago idan ta fal kwalla ta girgiza masa Kai.
Tace, "bansan su ba, kawai kama mutane suke yi inaga daba mu gudu bama Kiran Ku za'ayi ace Ku kawo kudi".
Baffa da Mujahid kallan ta kawai suke cike da mamaki taki yarda ma su hada Ido da su.
Abba yace, "Inaga masu garkuwa da mutane ne".
Daddy yace, "Bazaki iya tuna komai ba? Har inda suka kaiku?"
Hawayen da take makalewa ne ya zubo fuskar ta.
Tace, "abinda zan iya tunawa sanda kawai muka fito na taka Kaya daga nan ban kuma sanin ina nake ba kawai tashi nayi naganni anan".
"Waya kawoki".
Idon ta ta lumshe hawaye suka zubo mata sosai ta girgiza Kai tare da cewa.
"Bansani ba".
Abba yace, "ya za'ayi ace baki Sani ba? Ba tare aka sace Ku ba? Bakwa magana?"
"Bansani ba Abba ban tambayi sunan sa ba ban tambayi komai nasa ba".
"Amma Shi ya tambayi naki".
Daddy ya fada, bata da zabin da ya wuce eh hakan yasa.
Tace, "ehh ya tambaya".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...