47

80 11 0
                                    

*°🔘°A RAYUWAR MU°🔘°* 
     
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad @ *HijjartAbdoul.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗

.
*TUKUICI GA:* sweetheart

*SHAFI NA 47📑*

*__________📖* A hankali a hankali take bud'e idan ta har ta ware su tas a cikin wani d'aki kan ta taji yana sarawa ta tashi a hankali ta zauna tana k'arewa d'akin kallo kana gani zaka san d'akin mace ne, tashi tayi ta zauna tana cigaba da k'arewa d'akin kallo ganin irin dukiyar dake ciki, sai kuma ta fara tuna  abinda ya faru, ta shiga mota tana sauri bata san akayi ba taga mutum a bayan motar juyowar da zatayi ya zuba mata wani abu daga nan kuma shikenan bata ce me ya faru ba kuma a hankali ta tashi ta shiga toilet dan gabatar da sallahn da suka wuce ta ganin rana tayi sosai hakan ya bata tabbacin cewa gari ya waye.

Ta idar da sallah tana zaune tana tunanin wanne iri hali ahalin ta suke ciki taji an turo k'ofa an shigo d'ago da kanta tayi taga matar da ta shigo hannun ta d'auke da try fuskar ta cike da shu'umin murmushi d'auke kanta Mama tayi batare da ta nuna komai ba ta cigaba da abinda take har matar ta k'araso gaban ta ajje mata try d'in abincin sannan ta zauna tayi shiru, tana kallan Mama ganin de dagaske Mama bata da niyyar magana yasa ta cewa.

"Bazaki tambayi ya akayi kika zo ba?"

Shiru tayi mata batare da ta tanka taba.

"Ya kamata ace de at least  kin nuna damuwa amma banga alamar hakan ba".

Namma shiru bata tanka taba.

"By the way, ance kunne keji, to tunda wuri ki jawa yaran ki kunne basu da yara na akan wani tamilan d'anki, yaron ki yasa an kama yarana har biyu ko? nasan baza suji ba shiyasa na kama ki dan suji".

Mama batare da ta d'ago kan ta ba bare tasan tana yi sai dai tana jin ta.

"Madam Fatima kada ki damu idan kin fita bakiyi abinda na saki ba kinsan kema kina tare da wahala dan kuwa kina da 'ya Hajara kina da 'ya Maryam kina kuma da 'ya'yan 'yan uwa mata ki guji abinda zai faru dasu musamman wannan biyu naki zaki iya tafiya idan kin ci abinci motar ki a waje haka ma jakar ki mota".

Ta tashi ta tafi sai da taje bakin k'ofa taji Mama.

Tace, "Amma bake kika haifi yaran ki ba ko?"

Juyowa tayi tana kallan ta bata tab'a zatan wannan maganar ba, Maman ce ke tahowa wurin ta tana zuwa bata yi wata wata ba ta zabga mata mari.

"Wannan marin nasa iyali na a tashin hankali ne".

"Rana d'aya ki zama uwa ta gari kafin ki mutu ko zaki samu salama a zuciyar ki, zaki ji dad'in haka".

Daga haka kawai tasa kai ta wuce ta barta dafe da kunci cike da wani irin mamakin matar nan taya ma zata bar ta tafi? da sauri ta fito dan zuwa wurin ta tana fitowa taga Hainasu.

Tace, "Ohh nikam ankawo ni gidan jaraba da masifa harda bala'i ahe har sato mutane kike to wallashi bari Dad ya dawo na zayyana mahi komai da komai tunda de junan ki haka".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now