9

127 12 0
                                    


💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023









*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYEN NAH 🥰🤗🥰

*TUKUICI GA:* sweetheart😘

*SHAFI NA 9📑*

*__________📖* Tana zaune a parlour tana yin haddar ta Dan dukan su sun koma daki sun barta ganin haka yasa ta yin haddar ta tana nan zauen taga Mama da Daddy sun fito da sauri zasu fita tashi taje wurin su itama.

"Daddy waye ba Lafiya?"

"Patient aka kawo yanzu to ba kowa shine aka Kira Maman ki zan Kai tane na dawo".

"A can zata kwana".

"Ehh".

Mama tace, "wuce kije ki kwanta".

Ba musu ta kwashe kayan ta tayi sama tana sake  sake a ranta koda taje kwanciya kasa baccin tayi gaba daya tunanin sa ya addabe ta haka nan taji beda lafiya ganin tana hassaso Shi dakyar ta samu tayi bacci.

A asibiti kuwa Daddy Yana ajje ta ya dawo gida ita kuma ta shiga direct Emergency ya wuce da uniform din ta ta shiga anyi nasaran cire abincin da ya ci da ita aka karasa aikin.

Aka turo Shi suka fito, sai da ta tambayi doctors abinda ya same Shi.

"Yaci abinci ne Wanda aka sa masa poison".

"Poison?"

Ta maimaita,Yana cire hand gloves din sa.

Yace, "anje ayi test din wanne iri ne poison din yanzu de mun samu ancire abincin da yaci".

"Bari na duba lab din ko sun gama".

"Yawwa idan sun Gama ki taho dashi".

Tafiya tayi tana tunanin maganar su, yaro Karami amma ace ansa masa poison a abinci? Abin da mamaki sosai.

A hanya suka hadu da nurse din ta bata ita kuma ta koma bata Bude result din test din ba sai da taje ta Kai masa ya Bude.

Yace, "Tsaka ce ta Shiga abincin da yaci, please Mai dutyn dare bata zo ba ko zaki iya Kula da Shi?"

"Shikenan to ba matsala".

Fita tayi shima fitowa yayi yaje inda aka kwantar dashi, Iyayen ya yiwa biyani game da abinda ya same Shi sai anan suka dan ji relief Yana tafiya Hajjaty na aikowa da su dawo dan taga sun Mata wayar su babu yarda suka iya suka dawo babu kowa a wurin sa Sai Mama.

Mama na jinsu dayake bata fita ba zama tayi a wurin su, sai gashi ma an aiko ance  su koma meye dalili oho.

Washegari da safe ana zatan zai farka amma be farka Mama de na zaune ne tana jiran farkawar Shi amma shiru tasan alluran baccin da aka masa ce Mai Dan karfi shiyasa waya tayi wa Anty.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now