*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 36📑*
*__________📖* Jan mayafin ta tayi ta rufe fuskar ta jin kukan yak'i ya tsaya, har suka isa a kan kujera ta zaunar ta itama tana zama a kujeran kusa da ita.
"Sai aka ga damar kawo ta ko? ni ba mutum bace, ni ban isa ba da a fara kawo ta wuri na ba".
"Kiyi hak'uri HAJJATY". (🤔)
"Hauwa!"
Yarda ta faday Hauwar cikin fad'a shine ya kuma razana Siyama daman gashi tana kuka gashi kuma taji abinda aka fad'a akan ba'a kawo ta ba to Wacece?
"Hak'uri ne me? daman ai sai an cuceka ake baka hak'uri ko kin tab'a jin ina aka bawa mutum hak'uri haka nan kawai".
"Ina be k'ara baki hak'uri da kiyi hak'uri, wannan ita ce Maryam wacce aka aurawa..."
"Mashayi ba? d'an giya Allah yasa ta sani idan bata sani bama zata sani".
Sosai kukan idan ta ya k'aru yanzu d'an shaye shaye aka aura mata? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un gashi tana sanyin kuka da k'arfin tana jin tsoron abinda zaije ya dawo.
"Haba Hajjaty be kama ta kike wannan maganar haka, ki..."
"Bari na baki wurin tunda wa'azi kika fara".
Ya fad'a tana tashi,
"Sannan idan kun tashi tafiya keda mijin naki da kika gama sihircemin shi kada kuzo inda nake tunda ban isa ba an mayar ni bola".
Ya fad'a tare da barin wurin, dafe goshi tayi tare da sakin ajiyar zuciya sai yaushe ne zata gyara halin ta?, bud'e fuskar Siyama tayi tare da mata murmushi all is well tana share mata hawaye.
Tace, "kinga kada wannan ya dameki tashi inkai ki d'akin ki wanda shine naki".
"Bata da k'afa ko gurguwace, kin fad'a mata cewam arzik'i zata ci anan gidan? dan mijin ta banda zuwa club babu abinda ya iya da zuwa Gidan karuwai shine aikin harda sata ma yake yi ki fad'a duka wannan".
Ta fad'a tana wucewa kitchen, girgiza kai Mom tayi tana kallan Siyama data sunkuyar da kan ta hawaye na kuma zuba a idan ta.
"Kada shima ya dameki, ba haka yake ba, babu wanda ya tab'a zaunar shi ya fad'a masa abinda ya dace da kuma wanda be dace ba, abinda addinin mu ya k'unsa na tabbatar da be san muhimman abubuwan da ya kamata ace ya sani ba, ina so ki zama mace ta gari me sanin halin da mijin ta yake ciki, sannan zaki ji dad'in zama da shi na tabbatar da wannan".
Ta k'arashe da murmushi a fuskar ta.
"Bari na tafi idan tazo kada kiyi magana sai tace ki tashi ki tafi, kada ki gaidata, idan nazauna ni wani abin fad'ar ne".
"Nagode".
"Bakomai ki kwantar da hankalin ki".
Tana ta fita Hajjaty ta fito da bayan ta kuma 'yan aiki ne hannun su rik'e da kayan bucket masu murfi irin median dinan sai katan na taliya da su macaroni da sauran su a tsakiyar parlourn suka ajje suka juyawa inda suka fito.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...