*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 33📑*
*__________📖* Ita bata juyo ba ita bata amsa ba, a hankali ta fara tafiya batare da ta juyo ba, Mujahid ne da Baffa suka juyo ganin tana tahowa.
Mujahid yace, "Kije".
"Kuyi sallama".
Baffa ya fad'a da wata irin murya kamar shine zai rabu da ita, sai kuma ta tsaya ta dena binsu ganin haka da yayi yasa shi k'arasowa da sauri kamar zai fad'i.
Yace, "an fad'a maki nazo?"
Ya fad'a kamar mai tsoron fad'a yana kallan ta, d'aga masa kai tayi k'walla na cika idan ta.
"Kuka zakiyi?"
'Dagowa tayi tana kallan shi batasan sanda hawaye ya zubo mata, murmushin takaici yayi.
Yace, "yaushe ne?"
"Waya fad'a ma?"
Ta fad'a da hawaye na zuba sosai, shima kwallar yake sharewa a fakaice amma ganin hawayen ta yasa shi k'ara karyar masa da zuciya, murmushi yayi kuma mai ciwo.
Yace, "waya fad'a min lokaci ya k'ure Garrulous".
"Yaushe ne?"
Ya sake tambayar ta, sai da ta maida hawayen ta ta goge fuskar ta tare da folding hannun ta.
Tace, "Sati biyu".
"Yanzu..."
"Siyama dare nayi fa ki dawo haka".
Batare da ta kuma cewa komai ba ta juya da sauri gudu gudu ta shige cikin gida hawaye ne da yake boyewa ne ya zubo a idan sa ta tabbata kenan nan da sati biyu zata tafi.
A haka ta juya ya shige mota ya tafi yana tafe yana tunani har yaje gida, koda yaje Rufaida na nan bata tashi ba sai Hajjaty da Daada da suke zancen su shidai kawai ajjewa yayi tare da key yayi gaba batare daya ji abinda zata ce ba,bata tashi masa magana ba sai da taga ya bud'e k'ofar zai shiga.
Tace, "dayake uwar ka bata tab'a aiken ka bako? shine zaka je ka jima? uwar ka kayi a waje? wato ka samu freedom ba?"
Be juyo ba be kuma shiga ba har ta k'afar sa be sauke ba.
"Sai nace ka dawo zaka dawo ko? to dan uwar ka..."
Shigewa yayi ya bar ta da baki da sake.
Rufaida tace, "Uwar nan tasa fa ta riga da ta rasu, idan bazaki mata addu'a ba kawai kiyi shiru amma baki da aiki sai zagin uwar nan without realising that cewa kema uwa ce".
"Kana ji kana kallo tsabar an shanye ka 'yar ka na min rashin kunya kayi shiru".
Daada yace, "kiyi hakuri..."
"Dayake shi hakurin haka ake yin sa ko?"
Tab'e baki Rufaida tayi tare da bud'e ladern ta d'auka kaza d'aya tayi gaba tana cewa.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...