46

96 9 0
                                    

*°🔘°A RAYUWAR MU°🔘°*

*1442H/2020M.*

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad @ *HijjartAbdoul.*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* IYAYENAH 🤗😍🤗

*TUKUICI GA:* sweetheart

*SHAFI NA 46📑*

*__________📖* Ta tashi bata jin dad'i tunda suka tashi basu koma duk da baccin da yake ji amma ganin kamar ba normal take ba yasa yaji baccin ya b'ace masa sam beji gaba d'aya ya wani susuce da tambayar ta meke damun ta ita kuma amsa d'aya bakomai.

"Garrulous ki fad'a min, ko ki tashi muje asibiti".

"Bakomai fa nace maka normal ne".

"Kinsan bazan yarda ba, ko wannan sweat d'in da kika sha jiya shine ko?"

"Na manta ne yau ne jiya nasha shine".

"Meye kika manta yau ne?"

"OMG! Idan ka barni zanyi bacci ne".

Ajiyar zuciya yaja yana kallan ta cike da wani irin tausayi tayi tare da yin tagumi hannu biyu ita kanta ta rasa meke damun ta kawai haka taji bata jin dad'i duk da tasan idan zata yi period takan yi ciwon ciki ko ciwon kai da k'aramin zazzab'i shima befi kwana d'aya ba amma yau bata ji komai sai zafin jiki.

Kwanciya tayi tana lumshe ido ganin haka yasa shi shima kwanciyar yana kallan ta, kallan sa tayi tayi murmushi dole ta kuwa ta cire kunya ta masa magana idan ba haka ba zata aika ta wani abun kunyar ne.

"Cowardice?"

"Garrulous".

Ya fad'a yana shafa fuskar ta.

"Ko zakaje wurin Rufaida ka anso min pad?"

"Pad kuma? meye shi? me ake dashi?"

"Magani ne".

"Magani".

"Ehh, ko kafi so ka ganni a haka?"

"A'a Garrulous dena fad'a bari naje yanzu kiyi hakuri sannu".

Ya fad'a da sauri yana tashi da kallo ta juya tana ganin shi saura kad'an yayi tuntub'e ya fad'i lumshe idan ta tayi tana tunanin shi, shi wato bema san komai ba kenan.

Yana fita yayi part d'in su, besan d'akin ta ba, dan be tab'a shigowa ba sai dai idan zai shiga parlourn Daada shima befi sau kad'an ba, hakan yasa shi ya tsaya yana kissima ina ne d'akin ta wanda yake kallan shi ya nufa yayi knocking ba magana ya tura ya shiga gani yayi babu bedsheet alamar bakowa yau zata tafi k'ila ta wuce ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya juya ya fita aljihun sa ya tab'a yaga sauran 300 jiya yayi amfani da sauran kud'in da sauri ya fita dan zuwa shagon wurin layin su yana zuwa ya mik'a kud'in sa a bashi pad.

Mai shigon yace, "kud'in ka be kai ba".

"Ka bani ta kud'i na".

"Banda ita anan".

"To kayi hakuri ka bani sai na ciko maka Dan Allah sauri nake".

"300 fa ka bani, ni bamma san ka ba bare na ansa, dade ma ace 300 ne cikwan shine amma bazan ansa ba".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now