27

74 10 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 27📑*

*__________📖* Da tayi sallahn asuba ta koma ba ita tashi ba sai shadaya na rana, yau Monday ce dan haka babu kowa a gidan daga ita sai Baffa ko brush batayi ba ta sauko kai ba d'ankwali Baffa na zaune shima be jima da tashi ba tagan shi yana cin abinci ta karasa kawai tasa hannu ta fara ci wani banzan kallo ya wurga mata.

Yace, "wai ke meke damun? kin tashi kin bani wuri ko sai b'allaki".

Loma d'ayar da ta d'auka ta kai baki ta tashi tana gunguni tayi kitchen indomien daya dafa itama shi ta dafa ta soya k'wai ta daura shayi iya kofi daya sannan ta fito ko rabi abincin be ci ba sabida yana danna waya zama tayi a kusa dashi sai da ta fara ci.

Tace, "Ya Baffa wai gida nan yanzu madara aka dena sha kome? tunda nazo inaga bansha ba madara sai wasu su lemon grass wai sune shayi me za sumin? idan banda ramewa me zanyi?"

"Baki san hanyar shago ba?"

"Ai ta gida nake so kayan kwalama zanyi".

"Kinsa dakuwa zakiyi a wurin Mama".

Washe baki tayi.

Tace, "amma ai bata kwace wa ko? kaga duka ne kawai tana ina?"

"Inaga babu ko kin duba store babu?"

"A,a".

"Kada kuwa ki dameni tamn".

Shiru tayi tana cuno bakin ta.

Yace, "Daddy ya fad'a maki wanda yazo neman auren ki?"

"Wai Muzzaffar".

"Muzzaffar?"

"Haka yace sunan sa nidai bansan shi ba".

Shiru yayi yana kallan ta tana cin abincin ta babu abinda yake damun ta abin ma su yafi damun su shida Mujahid gashi ance Muzzaffar ne ji yayi abincin ya fice masa akai kawai wayar ya rike a hannu badan yana dannawa ba kawai hotan ta yake kallo ganin ta cinye nata.

Yace, "k'ara na k'oshi".

Karb'a tayi ta k'ara.

Tace, "hmm ni cin abinci na zan yi harda su nama kuwa, kaga ko daman idan na tashi aure ka fad'awa Daddy idan ba'a cin Nama kullum a gidan sa da kayan k'wala kada a bani shi ko ina san sa bare ma..."

Sai kuma tayi shiru bata k'arasa ba girgiza kai kawai yayi ya tashi ya fice daga gidan.

Abincin taji ya fice bata ta tashi taje ta rufe ta wanke abinda ta b'ata wanka tayi tare da brush ta fito ta shiga d'akin Daddy akan bedside drawer ta taga hotunan ta d'auko tana dubawa wasu bata gan su ba sai yanzu da take dubawa had'a hotunan sa tayi gaba d'aya tun yana jariri har ya fara rarrafe da sanda ya kai shekara goma duka ta had'a tana kallo sai kuma wanda sukayi da Baban su da Hajjo sai Abba da Daddy da ita dukan su suna dariya ita tana mamakin ma yarda ake suke hoto komai sai anyi masa hoto tana nan tana k'ara kallan hotan bata san da cewa lokaci yayi ba haka dan ko kira sallah bata ji ba sai da ta d'aga kai ta kalli agogon dake d'akin taje tayi sallah bayan ta kwashe hotan da ta d'auka nashi sai shida Maman shi guda d'aya, ajjewa tayi inda take ajje muhimman abubuwan ta sannan taje tayi sallah saukowa k'asa tayi dan d'aura abincin rana ta tarar da Baffa har ya girka yana kwashe wa k'arasawa tayi ta.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now