🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•**SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''
*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**When we are motivated by goals that have deep meaning, by dreams that need* *completion, by pure love that needs* *expressing, it is then when we truly live.*
*SHAFI NA 52📑*
*__________📖* k'arfe takwas Hajjo ta shirya tsab abin ta ta fito Mujahid tagani a zaune yana breakfast.
Yace, "Hajjo ina kwana?"
"Lafiya k'alau yi sauri ka gama kazo ka kaini gidan yarinyar nan".
"Hajjo da safe nan?"
"Zaka kaini ko kuma na kira uwarka ta kaini?"
"Zan kaiki amma gaskiya nikam ba yanzu ba ai kunya zaki sa naji nidai a'a".
"Kunya? ehh lalle ya tabbata na kuma tabbatar ashe abinda Hajjaju(Hajjon Gombe) take fad'a gaskiya ne akan ka, ni me kare maka ashe haka ne cabb".
"Ai gaskiya ce Hajjo yanzu meye abin zuwa gidan mutane kinga fa sai yanzu takwas da minti goma yayi ki bari idan na fito daga lectures sai na kaiki".
"Fatima, Fatima, Fatima".
Mama ce ta amsa tana daukowa.
"Karma ki k'araso koma ki d'auko hijabin ki da makullin mota ki kaini gidan yarinyar nan mai hankali da ladabi".
Mama tace, "ai Hajjo bansan gidan ba..."
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, baki san gidan ba, keda ba bafulatana ba ba komai ba? kice min baki san gidan ba kuna gari dayay a wannan zamanin bama zamanin ku ba lalle ne na k'ara tabbatar wa bakwa san ta".
"Hajjo bahaka bane bani da lokaci ne..."
"Kina da lokacin aikin ai, kinga saka d'anki tunda kin isa dashi ya kaini yanzu nan".
"Mujahid ka kaita Dan Allah kuma bansan k'ara jin wata maganar ta fito daga bakin ka".
"Tam".
Ajje abincin sa yayi ya tashi yana kumbura fuska ya d'auki jakar sa ya rataya yayi gaba, k'wafa tayi itama ta tafi Mama girgiza kai tayi ta koma.
Suna tafiya a mota kowa yayi shiru gashi ya kunna wak'a.
Tace, "Kai me ita 'yar uwar taka take so?"
Yasan idan yayi shiru to wata maganar ce idan yace sweet kuma to zasu tsaya.
Yace, "Kilishi".
"Aikuwa akwai wani mai kilishi can wurin..."
"Ba hanyar bace, gwara ki sai mata alawa tafi san ta".
"Tabbata, Allah shi kyauta".
Tsayawa yayi a bakin wani shago ta bashi dubu uku dayaje ya siyo mata kaluli ta 1500 dayawa ya rik'e sauran kud'in suka cigaba da tafiya.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...