14

93 12 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023






*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_ '''

Abu Qatadah (RA) reported: the messenger of Allah(SAW) was asked about the observance of saum (fasting) on the day of Arafa. (SAW) said, "''' *It is an expiation for the sins of the preceding year and the current year".* 

*SHAFI NA 14📑*

*__________📖* Saura kiris ta sauka Akan kafar ta kamar kiftar war Ido ya janye kafar ta aka maka masa a kafar sa, har ta rufe Ido tana jiran sautin Karan ya taba ta taji shiru gashi taji saukar kara, a hankali ta bude idan ta ta ware su fes a kan Shi beyi ihu ba sai runtse ido da yayi, kafar ta kalla ta kalleshi hawayen dake gudu a kan fuskar ta sune suka Kara gudu kawai taba Shi take ta kasa magana baan ta tashi zaune.

Mutumin yace, "Ke! Tashi ki koma dakin ki".

Bata ma San yana yi ba gaba Daya ta rude ta kasa tabuka komai sai kukan dake sauka a idan ta Yana diga a fuskar s.

Haushine ya ishe Mutumin yasa hannu ya danko Kan ta zai daga ta ta rike hannun Sameer gam tare da sakin ihu.

Buge Mata baki yayi.

Yace, "baza kiyi Shiru ba?"

Mizi ne ya Shigo bayan sa su Mad ne sai kuma wani wanda suke shigen kama da Mizi a bayan tafiyar sa ma ta fita daban a cikin su shima bayan sa masu take masa Baya ne su biyu hannun su rike da kujera irin ta bude wa nan sun rike ko daya.

Mizi yace, "Barde sake ta".

Sakin ta Barde yayi ya koma wurin kofa ya zauna shikuma aka bude musu kujera shida yayan sa suka zauna.

Yana sakin ta koma kansa Yana hawaye shikuma Jin azabar kafar ta dan ragu gashi de ita ke kuka amma ya Rasa dalilin da yasa yake Jin zafin abun a cikin zuciyar sa idan sa ya fara bude wa a hankali itama Shi take kallo suka hada girgiza Mata Kai yayi alamar a,a rufe bakin ta tayi da hannun ta tana daga masa ta kasa furta koda kalma Daya ce Kara damke hannun ta yayi dake cikin nasa sannan ya tashi dakyar ya jingina yana Jin radadin kafar sa na karuwa ta dalilin motsa ta da yayi ita kuma sai kallan sa take.

Su mizi na kallan su Basu ce komai ba  Dan su ba wannan ne a gaban su ba, sai dai kuma Yayan Mizi kallan Sameer kawai Yana kissima abinda zai masa.

Mizi yace, "Ke!"

Haryan zu hawayen take bata dena ba, sai da ta cire hannun ta daga Baki Jin ance ke ba da irin muryan Barde ba yasa su juyowa har Shi.

"Bamu da case da kai, amma ganin ka mutane na yasa kawai aka hada da Kai gudun bada shaida ke kuma".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now