💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.
Not Edited
POST 2020
REPOST 2023*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 11📑*
*__________📖* Ta gama shirin ta tsab tun 7 sai dai fargaban fita take ta hadu da Mujahid gashi ba kowa a gidan kowa ya kama gaban sa daman Hajjon Gombe bata tafi ba tana nan sai wani satin zata tafi hakan ba karamin samun relief tayi ba, ta shirya komai nata ta samu wuri ta zauna daga karshe ma chatting ta fara yi, sultan ne ya shigo.
Yace, "kut, daman kina ji mama na Kiran ki Ashe waya kike Dannawa ko?"
"Dalla can banji ba".
Ta fada tana ajje wayar sannan ta fita a hankali take tafiya har ta sauka ganin ba Mujahid yasa ta ajje ajiyar zuciya amma tuna wa da shine zai kaita makaranta yasa taji gaban ta ya fadi dakyar de ta tattara nutsuwar ta Shiga kitchen ta gaida Mama.
Mama tace, "a haka zakike zuwa makarantar ko?"
Cuno baki gaba tayi kafin ta sosa kanta ta darwaje Baki lokaci guda.
Tace, "bakomai fa bazan sake ba".
Kallan irin kedin? Mama ta mata sannan ta miko mata abinci suka fito tare a kasa ta baje suka zauna Mujahid ya fito ya gaida Mama Sultan ya gaida Shi Baffa Shi Basu koma ba shiyasa be fito ba Mama sai anjima zata tafi iya su uku ne ke breakfast Daddy daman Shi da wuri yake ficewa kasancewar sa ma'aikacin Banki.
"Ya Mujahid ina kwana".
Ta fada harda dan sunkuyawa dukda a zaune take.
Harara ya balla mata ya Mata kallan ni dake ne, be amsa ba hakan yasa ta kuma cewa.
"Ya Mujahid Nace fa ina kwana? Mama kinga de ina ta gaida Shi be amsa ba Kar a kuma cewa bana gaida su".
Sultan yace, "da yi kike? Yanzu ma wani Abu hala kike nema, kefa wata ran har Kiran sunan sa kike babu yaya".
"Allah Zan hada Ka da Hajjo taam".
"Kin jima bakiyi ba".
Shiru tayi tana cin abincin ta Kai kace da gaske shirun tayi ana jima wa ta fara magana tace wannan tace wannan Sultan Baya kulata har ya dawo yake Kula ta Mujahid kuwa hade girar Sama data kasa yayi Idan sun hada Ido ya galla Mata harara ita kuma tayi Kalar mutane salihai irin ba ruwa na din nan.
A haka suka Gama suka fita lokacin ana nema 8 saura, sultan sai Mita yake yi ta tsayar dasu dasu kadai ne da tuni sun tafi itade banza tayi dashi har sun fito ta kuma koma wa a dari ta canza Hajibi har kasa tasa safa ta saka Nikaf, ta fito ta Shiga Baya.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...