22

82 14 0
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1442H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

 

*SHAFI NA 22📑*

*__________📖* Bashi ya tashi ba sau karfe takwas a hankali ya bude idan sa ya sauke su akan hannun sa wanda ya damke d'an kwalin ta, tashi zaune yayi sannan ya bude d'an kwalin yana kalla yana tuna ta  tunawa da yayi beyi sallah ba yasa shi shiga toilet sai da ya fara yin wanka sannan ya fito shima wanka babu sabulu kawai da ruwa yayi ya fito rama sallan sa yayi sannan ya kwan ta a kasan yana tunani jin ya fara jin yunwa yasa shi tashi ya fita Hajjaty na zaune a parlour ta hikimce sam shi ya manta da kayan cin da ya dauka sun kare sai yanzu da ya fito ya tuna da sun kare.

Ko kallan ta beyi ba itama bata san zai kalle ta din ba ya wuce kitchen  rasa abin dauka yayi kawai ya dauko sabulu da klin ya fito har zai Shiga Corridorn da zai kaishi part din sa yaji tace.

"Sai a koma a ajje tunda ba ajiya kayi ba".

Numfashi yaja ya koma ya ajje ya dawo ya shiga dakin sa ya kwanta sam yana nan zaune yana tuna ta jefi jefi kuma yana yin murmushi juyi yayi ya dauka d'an kwalin ta yana juyawa a hannun sa  a haka baccin yunwa yayi gaba dashi.

Hajjaty na zaune tana jiran fitowar Daada dan yau tasan weekend ne babu inda zashi shiyasa bata kai masa breakfast ba idan ya fito yaci, tara kuwa da mintuna sai gashi ya fito. 

Gaisawa sukayi ta tashi taje ta kawo masa breakfast da kan ta, ta ajje masa agaban sa sai da yaci ya koshi yana neman tashi.

Tace, "Saddik".

Komawa yayi ya zauna.

Tace, "Shi wannan yaran haka za'a barshi yayi ta gantali kenan?"

"Hajjaty wanne yaro kenan?"

"Tashi ka bani wuri".

"Hajjaty bangane wanda kike fad'a ba shiyasa kiyi hakuri".

Cike da ladabi yayi maganar hakan yasa ta kalle shi ta kauda kan ta.

"Kaban wuri nace".

Be tashi ba sai ma kara dukar da kai da yayi sun jima a haka sosai can.

Tace, "wanne yaro ne idan ba wannan mashayin yaran ba kasan sarai shi nake nufi".

"Allah ya huci zuciyar ki".

"Amin".

"Yanzu me za'ayi? Ya kike gani za'ayi kenan?"

"Tunda ba karatun yake ba kawai ya koma gaban dangin sa na uwa nagaji da renon renon ya isa haka kuma".

"Amma Hajjaty bakya tunanin abinda zaije ya dawo?"

"Me zaije ya dawo? koma meye ya jima be je ba".

"Ina nufin ranar da suka ce zasu karbe shi sai baki yarda ba yanzu kuma..."

Shiru yayi ya kasa fadar abinda yake ransa yana so ya tuno mata abinda ya faru a ranar ne sai dai besan ta yarda zai ce ba shiyasa yayi shiru yana fadar abu zatace matar sa  ta koya masa rashin kunya kafin ta rasu.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now