🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU*
🤍🤍🤍
*1442AH/2020M•*®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•**SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''
*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘
Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**FROM THE TEACHINGS OF PROPHET MUHAMMAD (SAW).*
*Never hate each other: Never be jealous of each other: Never boycott of each other. Always remain brothers until each other...**SHAFI NA 51📑*
*__________📖* Ya tashi jikin sa da sauk'i sosai sai d'an abinda ba'a rasa ba yayin da ita kuma ta tashi da wani irin zazzab'i sai dai sosai ta b'oye shi sabida shi ganin idan ta yi masa sako sako bazai je ba aiki gashi kwana biyu beje ba kuma gobe Monday yake shirin komawa aiki dole ta zama matar auren gaske ba muna mata ba.
"Nifa yau Garrulous kinyi wani irin shiru nace zan zauna kince ba haka ba, sai naje nima banda lafiyan fa".
"Amma ai ka warke ba kamar jiya ba, dan haka kada ka makara kaje kayi aikin ka kayi da wuri sai ka dawo gobe Monday kuma zaka shiga school".
Dafe goshin sa yayi shaf ya manta stress d'in ya masa yawa dole yasan yarda zaiyi.
Tace, "Ka manta ko?"
"Wallahi kuwa".
"Ka tashi ka tafi tou".
Dawowa ya bud'e drawer ya d'auki kud'i duba d'aya.
Yace, "Idan kina da buk'ata ki d'auka ko kayan miya ko wani abu".
Da mamaki take kallan shi irin a'ina ka samu, ganin haka yasa shi matsowa ya kama fuskar ta yana kallan ta.
Yace, "Ranar dana je kasuwa shine aka bamu kowa 10k kin gane yanzu?"
D'aga masa kai tayi, rungumo ta yayi jikin sa yana sauk'e ajiyar zuciya.
Yace, "bansan tafiyar nan bakya jin dad'i ko?"
Breaking hug d'in tayi.
Tace, "ni k'alau nake, kada fa ka makara".
"To bye bye".
"Allah ya bada sa'a".
"Amin bye".
Yana fad'a ya wuce ya tafi tana gani ya tafi kuwa ta kwanta ta shiga bargo sai bacci.
Sallamar da taji an kwad'awa ne yasa ta tashi tare da zama sannan ta ta fito Ummi tagani a zaune tana kira waya, zama tayi.
Tace, "Ummi".
Ummi ta juyo.
Tace, "Ina kika shiga haka? nayi ta sallama shiru".
"Bacci nake tun d'azu wallahi bansan ma lokaci ya ja haka ba".
"Allah sarki dayake kwana biyu bakiyi ba".
"Da zazzab'i kuma".
"Allah sarki Allah sauwake".
"Amin, ba na kawo maki ruwa".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...