BARKA DA JUMA'A
Page 37
..................Sosai su Amaturrahman ke santin gidan Jawaad na A.Y Street, badan yafi kowane gidaba, bakuma dan an cikasa da ƙawa ba, ginine dai tamkar kowanne gini da kowa yasani, sai dai yanda akai tsarin gyaran sai ya kuma fiddo da ƙyawun gidan fiye da yanda yake a da, (masu karatu karku manta wannan shine gidan da aka haifa Jawaad, a cikinsa iyayensa suka rayu, dan shine gidannan da turawannan suka bama Abba Abdul-aziz, shine kuma sanadin wannan arziƙi daya tsolema mutane ido). Sai da suka shiga ko'ina da ina dan babu komai cikinsa sai ƙamshin sabon fenti.
Suna tsaka da dubawa Jay ya iso gidan, zaune yake a bayan motar sai Sadiq sabon drivern sa dake tuƙi cikin nutsuwa, dan shima dai baida matsala, amma hakan bai hana Jay tuna Gimba ba a kowacce daƙiƙa ta rayuwarsa, yasan gimba bazai mantu a zuciyarsa ba, dan yawuce duk tunanin mai hasashe a zuciyar tasa. Yauma kamar kullum yana cikin gayunsa da ƙyamshi, sai dai ya ɗan rame, hakan yasakashi yin wani fayau dashi, (bamu saniba azumin da aka shane kokuma ɗokin amaryarne. lol😂).
waya yakeyi, hakan yasa har Sadiq ya fito ya buɗe masa bai fitoba, sai da yaja kusan mintuna huɗu sannan ya fito bayan ya ajiye wayar, Safah data dage sai anzo da ita da gudu tayo kansa, fuskarsa ɗauke da murmushi harta iso garesa, hannunsa ta kama tana gaishesa. Shidai kallonta yake kawai, dan sosai ƙiriniyarta ke bashi mamaki, ko gajiya batayi, girma take amma abun tamkar ƙaruwar mata yakeyi. (Hhhhh tunda Jinin Munaya na yawo a jikin Safah ai kaga abinda yafi hakama, sarki Sameer ne zai baka labari dalla-dalla😂🤐). Cikin ɗoki tace, “Yayanmu gidanka kaida aunty B ya haɗu sosai, nima harna zaɓi ɗakina dan kasanfa nan zan dawo. Murmushi yay mata mai sanyi ya jinjina mata kai amma baice komaiba.
Sosai mamaki ya kama Jay lokacin da suka shiga ciki shi da Safah yay arba da Munubiya, shi tunaninsa Gimbiyace da kanta, itama ɗindai kallon mamaki take masan sai dai ita bamusan kona minene ba. Su Amaturrahman ne suka katse tunaninsa da gaisuwar da suke masa, ya amsa musu da kulawa kafin shima ya gaida Munubiya cikin girmamawa. Kasa haƙuri yay dai yace, “Ummu da kanki? Su Amaturrahman ma aisun isa basai ke kinzoba”. Munubiya tai murmushinta mai kama dana Munaya, kafin ta bashi amsa Safah tace, “Lah Yayanmu bafa Ummu bace, wannan Mami ce sweetheart ɗin Ummu”. Cikin rashin fahimta yake kallon Safah amma baice komaiba. Amaturrahman tace, “Yayanmu ai Ummu ƴan biyune, Mami itace hassanarta”. Ɗan waro idanu Jay yayi waje sai kuma ya shafa kansa, “Sorry Mami ai wlhy ni duk ɗaukata Ummu ce, bansan ita ƴan biyu baneba nasan dai tanada yaya mace”. “Karka damu ƙanina, Gida yay ƙyau masha ALLAH, ALLAH yasa rai akaimawa, ALLAH yasa a cika manashi taf da ƴaƴa ko jikoki zance”. Cikin murna su Safah suka shiga faɗin, “Amin”. Shidai a saman laɓɓa ya amsa nasa amin ɗin.
Kasa jurewa Mami Munubiya tai ta koma gefe tai kiran Munaya, tana ɗagawa tace, “Sweetheart kingako mina gani ga angon nan?”. Daga can murmushi gimbiya Munaya tai tana gyara kanta a kafaɗar takawa, tace, “Nasan ina kika dosa sweetheart, tun randa na fara ganinsa nima naga abinda kika gani, wannan ne dalilin tura matarsa can ta ɗan zauna, sai dai bamu da tabbas, amma muna fatan ALLAH yasa ta kasance hakanne”. “Kai to amin kuwa, al'amarin akwai ruɗarwa, amma gaskiya bana tantamar alaƙa a tsakaninsa da Umm-Anum Sweetheart, nifa da farko na zata Anuwar ne wlhy, sai da nai masa kallon nutsuwa na fahimci yafi Anuwar cikar zati, Anuwar kuma ya fisa haske, hatta da maganarsu kumafa babu banbanci, bara sai dai mun dawo ma tattauna”. Daga haka Mami Munubiya ta yanke wayar ta koma ciki dan baƙin da suke jira har sun iso.
Sai da suka gama zagaye gidan tsaf kafin su basu hotunan kayan ɗakin da zasu dace da tsarin gidan akan su zaɓa. Shi dai Jawaad bai saka musu bakiba, Mami dai ta tambayesa kalar da yafi so, ya sanar musu, daga haka ya cigaba da danne-dannen waya Safah na gefensa tana zuba masa surutu, shidai nasa saurarenta dayin murmushi, sai jefi-jefi yake bata amsar wani abun koyay mata tambaya.
Kusan awa guda suka kammala komai dangane da zaɓin kayan, a take Mami ta kira Ummu ta sanar mata kuɗin da suka cajesu. Kafin kuwa subar gidan har ƙuɗaɗensu sun shiga accaunt. daga haka suka bar gidan akan sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu zasu dawo suga yanda kamfanin suka shirya gidan. Jay yaymusu rakkiya har mota yanama Mami godiya, sai da suka wuce sannan shima ya shiga mota suka bar gidan.
YOU ARE READING
ƘWAI cikin ƘAYA!!
ActionTurƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wa...